KASSAROTA Ta Yi Hadin Gwiwa da Jami'an Tsaro Don Dakile Daukar Dabbobi da Mutane A Mota Daya.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes03092025_154759_FB_IMG_1756914360784.jpg



Auwal Isah Musa | Katsina Times 

Hukumar Kula da Harkokin Sufuri ta Jihar Katsina (KASSAROTA) ta gudanar da taron hadin gwiwa da jami'an tsaro da masu ruwa da tsaki a harkar sufuri, domin kawo karshen matsalar lodin wuce kima da kuma daukar dabbobi da mutane a mota guda daga jihar zuwa kudancin Nijeriya.

A jawabin da ya gabatar yayin taron hadin gwiwar, Daraktan KASSAROTA kuma Shugaban Hukumar, Manjo Garba Yahaya Rimi (Mai Ritaya), ya bayyana cewa an dauki wannan mataki ne bisa gaggawa bayan kungiyoyin UNION sun rubuta wa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, wasikar korafi kan matsalar.

Manjo Rimi ya ce, Gwamnan ya umurce su da su hada karfi da karfe tare da jami'an tsaro da hukumomin sufuri da sauran masu ruwa da tsaki wajen kirkirar "Taskforce Operation" domin lalubo hanyoyin magance matsalar.

Rimi, ya lissafo kasuwannin Charanci, Mashi, Dutsi, Mai'adua da Dandume a matsayin wuraren da aka fi samun korafe-korafen daukar mutane da dabbobi a mota guda zuwa wasu sassan kasar.

Ya kara da cewar, duk da kasancewar akwai dokar da ta haramta irin wannan dabi'a, akwai bukatar sake duba dokokin tare da yiwuwar gyara su a majalisar dokokin jihar domin samun mafita mai dorewa.

Bayan tattaunawa, hukumar KASSAROTA tare da jami'an tsaro da kungiyoyin sufuri sun samar da shawarwari 14 da za su mika wa gwamna domin daukar matakin da ya dace. Haka kuma, sun tsara jadawalin tarukan bibiyar ci gaban lamarin don tabbatar da nasarar shirin a fadin jihar.

A karshe, Manjo Rimi ya yi kira ga mahalarta taron da su yi aiki da gaskiya da adalci, tare da mai da hankali kan kare rayuka da dukiyoyin al'umma ba tare da son rai ba.

"Don Allah mu yi aiki tare da gaskiya da tsoron Allah, mu cire son rai, mu yi abin da ya dace domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummarmu," in ji shi, yana mai kammalawa da yi wa masu ruwa da tsakin nasiha.

Follow Us