Tattalin Arzikin Najeriya Na Samun Karin Daraja a Idon Duniya – Minista

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes13082025_155406_Alhaji-Mohammed-Idris.jpeg

Ministan Yada Labarai da Wayar Da Kan Yan Kasa, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya na samun yabo daga hukumomin kimanta tattalin arziki na kasa da kasa, wanda ke nuna karuwar amincewa da alkiblar da kasar ta dauka. Idris ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da Gwamnan Jihar Imo kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC, Hope Uzodimma, a Abuja. Ya ce shirin Renewed Hope Agenda na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu yana haifar da sakamako mai gamsarwa ga kasa.

A cewarsa, hukumomin kimanta tattalin arziki na duniya sun inganta ra’ayinsu game da Najeriya sakamakon ci gaba da ake samu a bangaren gyare-gyaren tattalin arziki da aiwatar da manufofi. Ya jaddada cewa duk da har yanzu ba a cimma cikakken buri ba, shirin gwamnatin na tafiya bisa tsari, kuma ana kan hanyar kaiwa ga burin cimma tattalin arzikin dala tiriliyan daya da Shugaba Tinubu ya yi alkawari.

Idris ya kara da cewa, ana samun ci gaba a fannin wadatar abinci da yaki da rashin tsaro, yayin da tsarin rabon kudaden gwamnati ke baiwa gwamnati a matakan tarayya da jihohi karin damar gudanar da ayyukan raya kasa.

Ya bayyana cewa ganawarsa da Uzodimma wani bangare ne na tuntubar juna tsakanin gwamnatin tarayya da ta jihohi don daidaita dabarun aiwatar da manufofin gwamnati. Ministan ya jaddada muhimmancin sanar da ‘yan kasa ci gaban da gwamnati ke samu, yana mai cewa aikinsa shi ne tabbatar da cewa jama’a sun san irin kokarin da ake yi don inganta rayuwarsu.

Follow Us