Al'ummar Mazabar Wakilin Gabas I Sun Mika Korafe Korafensu Ga Gwamnatin Jihar Katsina.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes07082025_175903_FB_IMG_1754589377242.jpg


‎Muhammad Ali Hafizy | Katsina Times. 
‎A yayin taron jin ra'ayin al'umma game da  kasafin kudi na shekarar 2026 da za'a yi, wanda mai girma gwamna Malam Dikko Umar Radda ya bayar da umarni akan kowace mazabu dake fadin jihar Katsina su bayar da rahoton abubuwan da suke bukata a yi masu idan an yi kasafin kudin.
‎Hakan ya sa shuwagabannin siyasa, da dattawa, masu rike da madafun iko, hadi da matasa maza da mata wadanda suke a yankin Gabas I dake cikin garin Katsina, suka gudanar da taron jin ra'ayin al'ummarsu a ranar Alhamis 07 ga watan Agusta 2025, a dakin taro ta "Multi-purpose Women Centre"
‎Kansilar mazabar wakilin Gabas I Hon. Zaharadeen Sirajo shine ya gabatar da taron maraba da al'ummar Mazabar, tare da yin kira ga shugabannin Mazabar da kuma dattawan mazabar akan su kasance gaba gaba wajen ganin sun samar ma Mazabar cigaba, dogaro da cewa Mazabar itace mazaba daya tilo da ta ƙunshi rumfunan zabe mafiya rinjaye a fadin Najeriya baki daya.
‎Baya da shi, dattijo daga Mazabar mai suna Alhaji Abdurrahman Marafa, shine ya fara jan hankalin al'ummar, akan su gabatar da bukatun al'umma ga gwamnati, ba wai bukatar mutum ya a kashin kanshi ba. Ya kuma yara da cewa, an kira taron ne domin al'ummar su fadi Korafe Korafensu da kuma rokon su ga gwamnati ga abinda suke ganin yakamata a yi masu.
‎Malam Munnir Badamasi C.S.O daya daga cikin shugabannin kwamitin karbar Korafe Korafen ya bayyana cewa, an samar da tsarin ne domin al'ummar su bayyana bukatunsu ga gwamnatin, domin ganin an shawo kan matsalolin al'ummar, da kuma tabbatar da an yi abinda al'umma ke su.
‎Ya kara da cewa Gwamna Malam Dikko Umar Radda shi ne ya kaddamar da wannan tsarin domin tabbatar ma al'ummar jihar Katsina da cewa wannan gwamantin tashi a shirye take domin samar ma al'ummar walwala tare da samar masu da dukkan abubuwan da suke bukata.
‎Shima Dr Mustapha Badamasi ya yi karin haske akan irin makarantun da yankin na Gabas I ya kunsa, tun daga kan Primary har zuwa Secondary, tare da bayyana irin makudan kudaden da gwamnati ta ware ma makarantun domin haɓɓaka su da kuma zaminantar dasu.
‎Daga jawabin Dr Mustapha Badamasi ne aka shiga kaitsaye wajen kiran wakilai daga dukkanin unguwanni da suke cikin yankin Gabas I din, domin gabatar da Korafe Korafensu da shugabanni taron da kuma al'ummar yankin nasu.
‎Daga karshe, shugaban taron kuma shugaban ma'aikata na jihar Katsina Alhaji Falalu Bawale, ya yi jinjina ga al'ummar Mazabar wajen amsa kiran gwamna da suka yi, tare da gabatar da Korafe Korafensu. Sannan ya tabbatar da cewa kwamitin karbar Korafe Korafen zai yi baki kokarin shi wajen isar da sakon.

Follow Us