An Bukaci a Binciki Takardun Dan Majalisar Musawa da Matazu Kan Zargin Takardun Bogi

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes23062025_101744_FB_IMG_1750673735918.jpg


Daga Katsina Times | 23 ga Yuni, 2025

Wani rahoto da aka wallafa a shafin jaridar Daily Trust a ranar Litinin, 23 ga Yuni, 2025 a shafi na 32, ya bayyana wata sanarwa daga wani mai suna Nuhu Muhammad Aliyu, inda ya bukaci a binciki takardun Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Musawa da Matazu, Hon. Abdullahi Aliyu Ahmed.

Sanarwar da aka biya kudin bugawa a matsayin talla ta zargi cewa akwai yiwuwar Dan Majalisar yana amfani da takardun da ba na gaskiya ba. Mai sanarwar ya nemi shugabancin jam’iyyar APC na kasa da su kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin zurfafa bincike kan zargin.

Haka kuma, ya bukaci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta gudanar da nata binciken kan sahihancin takardun da Hon. Abdullahi Aliyu Ahmed ya mika lokacin takarar kujerar majalisa.

Sanarwar ta kara da cewa gabatar da takardun karya babban laifi ne a kundin dokokin Najeriya, don haka yana da muhimmanci a dauki wannan batu da matukar muhimmanci domin kare mutuncin doka da tsarin dimokuradiyya.

Jaridar Katsina Times ta yi kokarin jin ta bakin Dan Majalisar kan wadannan zarge-zarge da suka fito a Daily Trust, amma kokarin bai yi nasara ba. Kiran wayarsa bai samu amsa ba, haka kuma sakon da aka aika masa bai samu martani ba. Hadiminsa a Majalisar Tarayya ma bai amsa kiranmu ba.

Za mu ci gaba da bin wannan batu domin samar da cikakken bayani ga al’umma yayin da abubuwa ke ci gaba da bayyana.

Katsina Times
@www.katsinatimes.com
Taskar Labarai
@www.taskarlabarai.com
Lamba: 07043777779

Follow Us