Salman Gafai Ya Jaddada Kudirinsa Na Siyasar Gaskiya Ba Da Gaba Ba

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes20062025_200859_Screenshot_20250620-210809.jpg

Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times

Fitaccen dan gwagwarmaya kuma jigo a siyasar yankin Yamma || da ke cikin birnin Katsina, Salman Ahamed Gafai, ya bayyana cewa ba zai daina fafutukar siyasa mai inganci ba, duk da kalubalen da ya fuskanta a baya. Ya bayyana hakan ne a wata hira da Katsina Times a ranar Juma’a, 20 ga Yuni, 2025.

Salman Gafai, wanda ya fito daga mazabar Yamma II a karamar hukumar Katsina, ya bayyana cewa tafiyar siyasarsa na dogara ne da tsarin gaskiya da kishin kasa, kamar yadda marigayi tsohon shugaban kasa, Malam Umaru Musa Yar’adua, ya assasa. Ya ce manufarsu ita ce yi wa jama’a aiki, ba neman wani riba ko biyan bukatun kai ba.

“Siyasa ba gaba ba ce. Ba don bukatun kanmu muke yi ba, sai dai don kare muradun jama’ar mu,” in ji Salman cikin kwarin gwiwa.

A yayin da yake bayani kan fitowarsa daga gidan gyaran hali a baya sakamakon wasu kalaman adawa da ya furta da suka fusata wasu 'yan siyasa, Salman ya ce hakan bai sauya masa ra’ayi ba. Ya ce yana da cikakken kwarin gwiwar ci gaba da fafutukar siyasa cikin tsafta da mutunta doka da oda.

“Za mu ci gaba da siyasa cikin gaskiya da tsafta ba tare da kaucewa ka’idojin dimokuradiyya ba,” a cewarsa.

Salman, wanda ya taba sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar SDP, ya bayyana cewa rashin cika alkawura da gaza bin tsarin da ya dace ne suka sa ya fice daga APC. Ya kara da cewa yana amfani da matsayin sa na dan siyasa wajen bijiro da bukatun al’ummarsa ga gwamnatin jihar Katsina.

Daga cikin bukatun da ya gabatar akwai batun gyaran titin filin Folo da wasu muhimman ababen more rayuwa da yankin Yamma II ke bukata. Wannan ne ya ja hankalin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, wanda ya gayyace shi domin jin ta bakinsa kan matsalolin yankin.

Salman ya bayyana cewa gwamnan ya nuna cikakken goyon baya, inda ya bayar da umarni ga hukumar kula da gyaran tituna ta jihar Katsina (KASSAROMA) da ta je ta duba yankin tare da daukar matakin da ya dace.

Shugaban KASSAROMA, Injiniya Surajo Yazid Abukur, tare da shugaban karamar hukumar Katsina, Honourable Isah Miqdad, sun tabbatar da cewa gwamnatin jihar tana cika alkawuran da take dauka.

“Gwamna Dikko Umaru Radda mutum ne mai gaskiya. Idan ya ce za a duba wani aiki, to kuwa za a duba shi. Ba ya yin alkawarin da ba zai cika ba,” in ji Engr. Surajo yayin duba wurin aikin.

Salman Gafai na daga cikin sabbin matasan da ke fitowa a siyasar Katsina da kudirin sake fasalin siyasa cikin gaskiya, adalci da kishin kasa. A yayin da yake ci gaba da bayyana ra’ayinsa cikin karfin hali, yana kara jawo hankalin masu ruwa da tsaki domin tabbatar da ci gaba mai ma’ana ga yankin Gafai da Katsina baki daya.

Follow Us