Auwal Isah Musa | Katsina TIMES
Wakilai daga gundumomin maza6u daban-daban na karamar hukumar Kaita, sun yi kira ga dan gwagwarmayar nan kuma jigo a kungiyoyin fararen hula na jihar Katsina, Kwamared Kabir Shehu 'Yandaki a kan ya fito takara domin ya wakilci kananan hukumomin Kaita/Jibia a Majalissar wakilan Nijeriya a zaben shekarar 2027.
Wakilan sun yi wannan kiran ne a ranar Talata, a yayin da suka yi tattaki daga yankunan nasu zuwa wajensa musamman don su bayyana bukatar.
Tun farko da yake jawabi, jagoran tafiyar, Lawal Rabi'u kwanaraye Dankaba ya bayyana cewar, a matsayinsu na wakilan mazabu daga karamar hukumar Kaita, suna bukatar ya fito ya wakilce su a majalissar wakilan Nijeriya na Kaita/Jibia; kiran da mutanen karamar hukumar Jibia suka fara yi kafin su.
"Mu ma yanzu mun zo ne mu ba ka shawara; don Allah ka karbi rokonmu, ka share mana hawayemu, ka ka fito takarar a majalissar wakilai!
"Mun zauna duka mazabun nan da yawun jama'a maza da mata, mun shawarta, mun ga ya dace ka fito takara domin ka wakilce mu ka kwato mana 'yancinmu. Don Allah kar ka ba mu kunya!" In ji su.
A cewarsu, dalilin da ya sa suke so ya fito takarar shi ne; "mun san tarihinka, mun san jajircewarka da irin gwagwarmayarka, mun kuma san muhimmancinka da irin ayyukan alherin da ka rika yi a karamar hukumar Kaita."
Da yake mai da jawabi, Kwamared Kabir Shehu 'yandaki ya yi godiya ga tawagar wakilan bisa ga tattakin da suka yo don bayyana bukatuwar tasu, inda ya bayyana kiran nasu a matsayin maimaici a kan na wasu, domin mutanen karamar hukumar jibia su ma sun zo a kan hakan.
"Wannan kiran ba shi ne na farko ba, mutanen jibiya sun yi ta kira a kan takara, tun watannin baya nake ta amsa kiran waya kan haka." Ya bayyanar
Ya ce, kiran farko da aka yi masa akan batun, ya tsawatar ne da hani a kan hakan, amma a cewarsa daga baya mutane jibia suka yo takakkiya wanda hakan ya sa dole ya saurare su, daga nan ya ce zai yi shawara da manya don siyasa ba a yi?mata kundunbala.
Kwamared 'Yandaki ya ce masu a yanzu dai shi da iyayen gidansa a siyasa ba su da jam'iyya tukunna, sai dai ya ce nan da 'yan kwanaki kadan za su bayyana jam'iyyarsu wanda a kanta shi kuma zai yi takarar da suka bukace shi ya fito.
Daga karshe, Yandaki ya bayyana Dr. Mustapha Inuwa a matsayin jagorransu a siyasa, inda ya jaddada cewar duk jam'iyyar da suka fitar ita ce zabinsa, kuma a cikinta zai tsaya takarar da suka kiraye sa ya yi.
Gundumomin da wakilan mazabun suka fito suka nuna bukatar tsayawar tasa takara sun hada da: Ba'awa, 'Yandaki, Abdallawa, Dankama, Matsai, Kaita, Dankaba, Gafia da sauransu.