Shekaru 22 Rimi Na Cikin Maraici!
Daga Hassan Abdu, Rimi
Kwanakin baya Sarkin Katsina Abdulmumini Kabir Usman ya yi wani jawabi inda ya bayyana cewa "Katsinanci na nufin Baƙin ciki" mutane da yawa sun Ƙalubalance shi amma ba wai don basu yadda da abinda ya fada ba ne, sai dai kawai domin bayar da kariya ga garinsu da al'ummarsu a idon duniya, amma sun yi imani da abinda Sarkin ya fada gaskiya ne.
Na yi wannan tsokacin ne domin abinda zan yi magana kansa dangane da kujerar majalissar Tarayya ta Rimi/Charanchi/ Ɓatagarawa (RCB). Bayan dawowar Damakuradiyya a shekarar 1999 ƙaramar hukumar Rimi ita ta fara jagorantar wannan kujerar na tsawon wa'adi guda, wanda kullin wasu ke kawo cikas inda haka ya sanya kujerar ta bar ƙaramar hukumar Rimi
Tun daga wannan lokacin ƙaramar hukumar bata sake samun wannan damar ba sakamakon wasu dake ganin sune jigon siyasar karamar hukumar kuma in ba su ba to kowa ma ya rasa. Ba sa kishin karamar hukumar kawunansu kawai ke gabansu, har zama aka yi aka yi tsarin karɓa-karɓa, amma waɗannan mutanen da ke ganin cewa in ta dawo Rimi za su rasa damarsu, suka riƙa sayar da ita ga sauran ƙananan hukumomin Charanchi da Ɓatagarawa.
Karamar hukumar Rimi na buƙatar wannan kujerar ne saboda samun damar inganta ƙaramar hukumar ta ɓangarori da dama. Amma su waɗannan mutanen su ne kullum kan gaba wajen watsa wannan shirin saboda su kawai kansu suka sani ba sa kallon ƙaramar hukumar da cigabanta.
Babban abinda zai baka mamaki yadda wanda ake ganin shi ne 001 a karamar hukumar Rimi amma kuma a wasu taruka da aka yi baya aka jiwo shi yana tallata wannan kujerar ga wata ƙaramar hukuma ba Rimi ba.
Yana da kyau masu ruwa da tsaki na wannan ƙaramar hukumar Rimi su jawo hankalinsa su gwada masa shi shugaba ne, kuma ya maida ƙaramar hukumar gabansa kuma ya sani cewa bai kamata ya sa wata ƙaramar hukuma gaba ba ga tasa in dai har yana kishin Rimi.
Domin in a da ba shugaba ba ne, ba shi ake ko kuma so yake a gina shi, to ya sani yanzu shi zai gina kuma shi zai bayar kuma tarihi ba zai taɓa mantawa da shi ba, na abinda zai yi na gina ko rusa Rimi da al'ummar ta ba.
Kazalika, shi ma tsohon shugaban ƙaramar hukumar kuma tsohon mataimakin kakakin majalissar dokoki na jihar Katsina ya shirya wani taro na magoya bayansa inda ya bayyana masu cewa, sun amince da tafiyar RBC a kakar zaɓe ta 2027 ta cigaba kamar yadda ya saba saida ƙaramar hukumar a zaɓukan baya.
Duk da dai gidajen jaridun da suka ruwaito rubutun daga baya sun masa kwaskwarima. To abinda ya kamata ya sani cewa shi ɗan ƙaramar hukumar Rimi ne kuma shugaba bai kamata ba irin wannan subil da baka ta fito daga bakinsa, ba wanda ya hana shi ya yi ra'ayinsa amma dai ya sani ƙaramar hukumar Rimi da cigabanta na gaban kome.
In ma wasu kuɗaɗen aka bayar domin yin irin waɗannan zantuka ga shugabannin ƙaramar hukumar Rimi to ya kamata su dawo hayacinsu, domin tallakawa na kallonsu, kuma sun san su waye su, kuma suma suna da ra'ayin kansu na cigaban ƙaramar hukumar Rimi. Kuma idanuwansu buɗe suke dan an cicciramasu wasu 'yan kuɗaɗe hakan ba zai sa su ɗauki mataki a rumfunan zaɓe ba.
Daga ƙarshe za mu yi kira ga al'ummar ƙaramar hukumar Rimi musamman waɗanda aka kawo fuskokinsu domin a saida su da su. Kuma suma suna da ra'ayin kansu na cigaban ƙaramar hukumar Rimi domin idanuwansu a buɗe suke.sannan suna kallon marasa kishin ƙaramar hukumar Rimi da yanzu Allah ke nuna masu su a fili.
Wannan ra'ayina ne, domin an ce ra'ayi riga kowa da irin na sa. Saboda haka kofa a buɗe take wajen bayyana gaskiya dangane da makomar siyasar Rimi a hannun waɗannan mutane.