Gwamnatin Jihar Katsina Ta Ba Da Hutun Babbar Sallah Ga Makarantu Daga 4 Zuwa 11 Ga Yuni, 2025

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes30052025_180509_FB_IMG_1748628210053.jpg

Daga Wakilinmu,

Ma’aikatar Ilimi ta Firamare da Sakandare a Jihar Katsina ta sanar da cewa dukkan makarantun gwamnati, masu zaman kansu da na al’umma za su tafi hutun Babbar Sallah daga ranar Laraba, 4 ga Yuni, 2025, tare da komawa makaranta a ranar Laraba, 11 ga Yuni, 2025.

Sanarwar ta fito ne daga ofishin Daraktan Makarantun Sakandare (JSS), Kabir Dodo, wanda ya sanya hannu a madadin Kwamishiniyar Ilimi, a wata wasiƙa mai kwanan wata 30 ga Mayu, 2025, mai taken: “Notification on Eid-al-Kabir Sallah Break and Closure of Schools.”

A cewar wasiƙar, an umurci dukkan makarantun jihar da su kiyaye wannan jadawalin hutu tare da bin umarnin da aka bayar cikin wasiƙar.

"An umurce ni da in rubuta in sanar da ku cewa dukkan makarantu za su tafi hutun Babbar Sallah daga ranar Laraba 4 ga Yuni, 2025, sannan su koma makaranta ranar Laraba 11 ga Yuni, 2025,” in ji sanarwar.

Haka kuma, an bukaci makarantu masu zaman kansu da na al’umma su tabbatar da bin wannan umarni.

Sanarwar ta kuma yi fatan alheri da barka ga malamai da ɗalibai a lokacin shagulgulan Babbar Sallah.

Follow Us