Ɗaura Aure ba tare da Shedar Likita ba yaci Rawanin Hakimi a Katsina.
- Katsina City News
- 18 Sep, 2023
- 1055
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Kamar yanda Takardun Dakatar war guda biyu suka bayyana ɗaya daga Fadar Gwamnatin jihar Katsina mai ɗauke da sanya hannun Daraktan Yaɗa Labarai na Sakataren Gwamnatin jihar Katsina wanda aka rabawa Manema Labarai, ɗaya takardar kuma na ɗauke da sa hannun Sakataren Masarautar Katsina.
Sun bayyana Dalilan Dakatar war bisa zargin Sarkin Kurayen Katsina Hakimin Gundumar Kuraye da Jagorontar Daura Auren Alh. Lawal Mamman Auta da Hajiya Halimatu Abdullahi Kuraye, wanda takarda ta bayyana cewa ya sabawa Doka a dalilin rashin Gwajin tabbatar da lafiya ma'auratan, inda takardar ta bayyana zargin dayansu yana Dauke da kwayar cutar HIV.
Kamar yanda Sanarwa ta bayyana cewa dakatar war ta fara aiki nan take.
Abubakar Abdullahi Amadu Hakimin Gundumar Kuraye a Karamar hukumar Charanci ya shekara kusan goma sha bakwai 17 a Sarautar Kurayen Katsina, wanda Mai marta marigayi Sarkin Katsina Muhammadu Kabir Usman ya naɗashi kafin rasuwar sa, a shekarar 2007 inda ya gaji mahaifinsa Marigayi Abdullahi Amadu Sarkin Kuraye na I