CP Bello Shehu Ya Karɓi Kungiyar Matan 'Yan Jarida ta Ƙasa a Ziyarar Ban Girma

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes22052025_192702_FB_IMG_1747941964057.jpg

Maryam Jamilu Gambo | Katsina TIMES 

Kwamishinan Ƴan Sanda na Jihar Katsina, CP Bello Shehu, psc, fdc, MNIM, ya karɓi bakuncin membobin Kungiyar Matan 'Yan Jarida ta Ƙasa (NAWOJ) a ziyarar ban girma da suka kai masa a ofishinsa ranar Alhamis, 22 ga Mayu, 2025.

Shugabar kungiyar ta jihar Katsina, Hajiya Hannatu Mohammed, ita ce ta jagoranci tawagar. A cikin jawabin da ta gabatar, ta taya kwamishinan maraba da saukar aiki a jihar tare da bayyana jin daɗin zumuncin da ke tsakanin 'yan jarida da rundunar ‘yan sanda a jihar. Ta nemi ci gaba da haɗin gwiwa domin inganta isar da sahihan labarai da kuma ƙarfafa wayar da kan jama'a.

Hajiya Hannatu ta kuma roƙi Kwamishinan da ya duba yiwuwar tallafa wa kungiyar, musamman wajen yaƙi da cin zarafin mata da sauran ƙalubale da ke addabar mambobinta.

A nasa bangaren, CP Bello Shehu ya bayyana godiyarsa ga ziyarar da NAWOJ ta kai, tare da yaba wa rawar da kungiyar ke takawa wajen inganta ɗabi'ar aikin jarida. Ya tabbatar da aniyar rundunar wajen ci gaba da kyakkyawar alaƙa da ‘yan jarida tare da shawararsu da su riƙa tantance bayanai kafin wallafawa.

“Muna da niyyar ci gaba da ƙarfafa dangantaka mai kyau da kafafen yaɗa labarai, domin jin daɗin jama’ar Jihar Katsina gaba ɗaya,” in ji CP Bello Shehu.

Game da ƙorafe-ƙorafen da shugabar kungiyar ta gabatar, CP Bello Shehu ya bayyana cewa rundunar na daukar matakai tun da farko domin dakile matsalolin cin zarafin mata da sauran batutuwan da suka shafi mata da kungiyar baki ɗaya.

An kammala ziyarar da ɗaukar hoto tare da ƙungiyar a matsayin alamar haɗin kai da fahimtar juna.

Hotunan Rundunar 'Yansandan jihar Katsina

Follow Us