Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Ummi Taibat Yakubu – Katsina Times
Gwamnatin Jihar Katsina ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace domin tabbatar da jin daɗi da walwalar alhazanta a aikin Hajjin bana na shekarar 2025, a cewar Amirul Hajji kuma Mataimakin Gwamna, Malam Faruq Lawal Jobe.
A cikin wata tattaunawa ta musamman da ya yi da Katsina Times a ranar Talata, 20 ga watan Mayu 2025, a ofishinsa da ke tsohon gidan gwamnati, Sa’idu Barda House, Jobe ya bayyana cewa aikin Hajji ibada ce da ake gudanarwa duk shekara, don haka gwamnati a kowane lokaci tana hada kai da Hukumar Jin Daɗin Alhazai domin inganta yadda alhazai ke gudanar da ibadarsu cikin sauki.
Dangane da kula da lafiya, Jobe ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta tura likitoci guda bakwai tare da sauran ma'aikatan jinya zuwa ƙasar Saudiyya domin kula da lafiyar alhazai, musamman wajen dakile cututtuka da kuma magance matsalolin lafiya cikin gaggawa. Ya ce wannan adadi ya wuce ka’idar da aka saba, wanda ke nuna kulawar gwamnati wajen ganin lafiyar alhazanta ba ta samu cikas ba.
Game da bangaren addini, Jobe ya ce an tura malamai mata da maza daga kowace ƙaramar hukuma guda biyu, tare da kafa kwamitin malamai na jiha domin gudanar da wa’azi da ilmantarwa ga alhazai kan abubuwan da suka dace da wadanda ya kamata a kauce musu domin samun hajji karbabbe.
Kan batun jigilar kaya, Jobe ya bayyana cewa an tura ma'aikata na musamman da za su taimaka wajen daukar kayayyakin alhazai daga Najeriya zuwa Saudiyya. Wannan mataki, a cewarsa, zai rage musu wahala da nauyin da ke tattare da jigilar kaya.
Ya kara da cewa tawagar Amirul Hajji ta kunshi mutane 14 ciki har da wakilan sarakuna, ‘yan majalisa, malamai da sauran kwararru. Jimillar mutane 174 ne gwamnati da kananan hukumomi suka dauki nauyin tafiyarsu domin taimakawa alhazai wajen sauke nauyin ibadarsu yadda ya kamata.
Jobe ya bayyana cewa ya yi wa alhazai jawabi kafin tashinsu inda ya ja hankalinsu da su mai da hankali kan ibada da kula da kudinsu. Ya bukace su da su guji masu damfara tare da yin amfani da wuraren canjin kudi da gwamnati ta amince dasu don kaucewa asara, duba da cewa kudaden da ake amfani da su a wajen ba na gida ba ne.
Haka kuma, ya bayyana cewa Gwamna Malam Dikko Umar Radda ya bada gudummawar Riyal 600 ga kowane alhaji domin saukaka musu wajen sayen dabbar hadaya, lamarin da ya rage radadin kashe kudi ga fiye da alhazan 2000 da jihar ke da su a bana.
Jobe ya ce an tanadi masaukai masu kyau ga alhazai, kuma an tabbatar da cewa kowanne jirgin da zai dauki alhazai yana dauke da wakilan gwamnati domin lura da hakkokin alhazai. Ya ce ba za a bar kowane alhaji ya tafi ƙasa mai tsarki ba tare da shugabanni da masu lura da bukatunsa ba.
A ƙarshe, Amirul Hajji ya bukaci alhazai da su rika yin addu’a don samun hajji karbabbe da kuma zaman lafiya mai dorewa a Jihar Katsina da ƙasa baki ɗaya. Ya ce gwamnati ta tsara komai yadda ya kamata, sai kawai a tabbatar da aiwatar da shirin cikin tsari da daidaito.