Gwamnatin Jihar Katsina Za Ta Karɓi Bakuncin Taron Bajekolin Kirkira Da Fasahar Zamani "Arewa Tech Fest"

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes19052025_165520_FB_IMG_1747673648313.jpg

Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Time, 19 ga Mayu, 2025 – 

Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da shirinta na karɓar bakuncin baje kolin fasahar zamani na Arewa Tech Fest 2.0 daga ranar 20 zuwa 22 ga Mayu, 2025, a cibiyar taruka ta Continental Event Center da ke cikin birnin Katsina.

Wannan sanarwar ta fito ne daga kwamitin shirya taron a madadin gwamnatin jihar da Hukumar Fasaha da Sadarwa ta Zamani ta Jihar Katsina (KATDICT), inda aka bayyana cewa wannan taro zai tara manyan masu fasaha, masu kirkire-kirkire, masu zuba jari, masana, da masu tsara manufofi don haɓaka ci gaban fasaha a Arewacin Najeriya.

Bayan nasarar da aka samu a taron farko da aka gudanar a Kano, an shirya Arewa Tech Fest 2.0 domin ƙarfafa sabbin dabaru da haɗin gwiwar da za su taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin yankin ta hanyar amfani da fasahar zamani.

A ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dikko Umaru Radda, Jihar Katsina na canzawa daga tattalin arzikin noma zuwa wani sabon tsari na tattalin arzikin zamani mai dogaro da ilimi da fasaha. Gwamnan ya himmatu wajen ganin cewa kowa ya samu damar amfani da fasahar zamani, da kuma koyon ilimin zamani da kirkire-kirkire ba tare da wata tangarda ba.

Sanarwar ta ce, “Shirin Gwamna Radda na juyin juya halin fasahar zamani ya haɗa da buɗe ƙofofin ci gaban matasa ta hanyar ba su kayan aiki da horo da za su taimaka musu su yi fice a duniyar zamani.”

Wasu daga cikin nasarorin da aka cimma a ƙarƙashin jagorancin gwamnan sun haɗa da:

Farfaɗo da hukumar KATDICT don zama ginshiƙin ci gaban fasaha a jihar

Cire kuɗin izini (Right-of-Way) domin sauƙaƙa shimfiɗa layukan sadarwa

Faɗaɗa cibiyoyin sadarwa don ƙara sauƙin samun intanet

Zuba jari a fannin koyar da fasahar zamani da horar da matasa

Katsina na ƙara zama abin koyi a Arewa wajen tsara manufofin ICT, gina ababen more rayuwar zamani da kuma samar da tsarin shugabanci na kirkire-kirkire.

Taron na bana mai taken “Kirkire-Kirkire Don Tasiri – Fasaha a Matsayin Maƙasudin Juyin Juya Halin Tattalin Arziki” zai zama wata dama ta haɓaka kirkire-kirkire, zuba jari da haɗin gwiwa tsakanin bangarori daban-daban na ci gaban yankin.

A cikin kwanaki uku, za a gudanar da jawaban kwararru daga cikin gida da ƙasashen waje

Tattaunawa kan sabbin fasahohi, manufofin dijital, da tallafin jarin ƙanana da matsakaitan kamfanoni

Taron bita da gasa don warware matsalolin cikin gida ta hanyar fasaha

Nuna ƙirƙira da kayayyakin da matasa daga Arewa suka samar

Taron haɗin gwiwa tsakanin matasa da masu jari da masu ba da shawara

Taron zai bai wa matasa da ƙananan kamfanoni damar samun dama ga kasuwanni na duniya, jawo hankalin masu zuba jari zuwa yankin, da kuma samar da guraben ayyukan yi a sabbin masana’antu.

Har ila yau, zai taimaka wajen haɗa al’ummomin karkara da duniyar zamani ta hanyar sadarwa, da ƙarfafa haɗin gwiwa a tsakanin jihohin Arewa a fannonin fasaha da ci gaban tattalin arziki.

Gwamnatin Jihar Katsina ta buɗe ƙofa ga ‘yan kasuwa, masu zuba jari, cibiyoyin gwamnati, jami’o’i, ƙungiyoyin cigaba, da jama’a gaba ɗaya da su halarci wannan taro mai muhimmanci.

“Arewa Tech Fest 2.0 ba kawai taro ba ne, babban mataki ne na kafa tubalin makomar zamani mai cike da cigaba, adalci, da haɗin kai a yankin Arewa,” in ji sanarwar.

Follow Us