GWAMNA LAWAL YA ƘADDAMAR DA KWAMITIN KULA DA AIKIN HAJJIN 2025, YA JADDADA BUƘATAR KAUTATA JIN DAƊIN ALHAZAN ZAMFARA

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes13052025_142507_Lawal.webp


Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ɗora wa Kwamitin Kula da Aikin Hajji Na 2025 alhakin tabbatar da jin daɗin alhazan jihar baki ɗaya a yayin da suke gudanar da aikin Hajjin bana.

A ranar Laraba ne aka ƙaddamar da kwamiti mai suna 'Amirul Hajj' na Jihar Zamfara na shekarar 2025 a gidan gwamnati da ke Gusau.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa Mai Martaba Sarkin Maradun, Alhaji Garba Muhammad Tambari, zai kasance Amirul Hajj na 2025 kuma shugaban kwamitin.

Kwamitin ya kuma haɗa da Honarabul Sulaiman Adamu Gummi, Kwamishinan Al’amuran Addinai, wanda ke riƙe da muƙamin mataimakin shugaba, sai kuma Alhaji Habibu Balarabe, Babban Sakataren Hukumar Zakka, a matsayin sakatare. 

Yayin ƙaddamar da kwamatin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa ana sa ran tawagar za ta tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin nasara da walwala, aminci da jin daɗin alhazan Jihar Zamfara.

“Gwamnatin Jihar Zamfara, a madadin al’ummarmu, ta ba ku kwarin gwiwa sosai wajen ganin an aiwatar da kowane fanni na aikin Hajjin 2025 cikin inganci, mutunci, da gaskiya.

“Ina kira gare ku da ku ci gaba da ƙulla kyakkyawar alaƙa da Hukumar Alhazai ta Jihar Zamfara, da hukumomin Tarayyar da abin ya shafa, da kuma abokan hulɗar mu na Saudiyya, domin tabbatar da samun haɗin kai da warware matsalolin da suke faruwa a zahiri, dole ne ku rungumi hanyoyin tausayawa a cikin dukkan harkokin ku, da sanin cewa rayuwar ɗaruruwan ‘yan jihar na hannun ku.

“Gwamnatin jiha, Insha Allahu, za ta bayar da dukkan goyon bayan da suka dace domin ganin an sauke nauyin da aka ɗora muku yadda ya kamata, muna sa ran samun rahotannin ci gaban a kan lokaci, kuma a ƙarshen aikin hajjin za a fitar da cikakken rahoton da ya ƙunshi nasarori, ƙalubale, da shawarwarin manufofin gudanar da aikin hajji a nan gaba.

“Ku jakadu ne na Gwamnatin Jihar Zamfara da al’adunmu, da ɗabi’unmu, da mutuncin addininmu a duniya, don haka ina roƙon ku da ku nuna kyawawan halaye na tawali’u, haƙuri, ɗa’a, da sadaukarwa a duk tsawon wannan aiki, ku bar halinku ya zama abin koyi ga sauran mutane.”

Follow Us