Shugaban Rikon Kwarya na Guinea, Mamady Doumbouya, a cikin Rayuwa da Mulki

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes09052025_200955_FB_IMG_1746821353527.jpg


Zaharaddeen Ishaq Abubakar 

Mamady Doumbouya, wanda ke jagorantar gwamnatin rikon kwarya a kasar Guinea tun bayan juyin mulkin 2021, ya fito daga yankin Bananköröda a jihar Kankan, inda aka haife shi a ranar 4 ga Maris, 1980.

Doumbouya ya fara karatunsa a cikin gida Guinea, kafin ya samu horo na soja a kasashe da dama ciki har da Senegal, Gabon, Isra’ila da Faransa. Ya halarci makarantar horon sojoji ta École de Guerre da ke birnin Paris, kuma yana da digiri na biyu a fannin tsaro da dabarun masana’antu daga Jami’ar Paris-Panthéon-Assas. Haka kuma, ya yi horo na musamman a fannin tsaro da kariya a Isra’ila, tare da samun horo na kwamandoji a wasu kasashe daban-daban.

Kafin dawowarsa gida, Doumbouya ya yi aiki da rundunar French Foreign Legion inda ya halarci wasu muhimman ayyuka a kasashen Afghanistan, Côte d’Ivoire, Djibouti da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. A shekarar 2012 ya dawo Guinea, kuma zuwa shekarar 2018 aka nada shi shugaba na rundunar Special Forces Group (GFS) wacce ke da alhakin yaki da ta’addanci. A wannan matsayi ya yi kokari wajen zamanantar da rundunar tare da kara mata 'yancin aiki.

A ranar 5 ga Satumba, 2021, Doumbouya ya jagoranci juyin mulki da ya kifar da tsohon shugaban kasa Alpha Condé, inda ya ce gwamnatin ta lalace, tana cin hanci da rashawa, kuma tana tauye 'yancin dan Adam. Bayan juyin mulkin, Doumbouya ya rusa gwamnati, ya dakatar da kundin tsarin mulki, tare da kafa kwamitin mulki na rikon kwarya mai suna National Committee of Assembly for Development (CNRD).

A ranar 1 ga Oktoba, 2021, an rantsar da Doumbouya a matsayin shugaban rikon kwarya. Ya yi alkawarin sake rubuta kundin tsarin mulki, ya yaki cin hanci da rashawa, da kuma shirya sahihan zabuka. A da farko sun ayyana cewa mulkin na rikon kwarya zai dauki watanni 39, amma daga baya aka takaita zuwa shekaru biyu saboda matsin lamba daga kasashen waje. Duk da haka, har zuwa farkon shekarar 2025, ba a kammala tsarin komawa mulkin farar hula ba, sai dai an tsara gudanar da kuri’ar raba gardama a kan sabon kundin tsarin mulki a watan Satumba 2025.

A lokacin mulkinsa, Doumbouya ya dauki wasu matakai da suka hada da tilastawa kamfanonin hakar ma’adanai na kasashen waje su gina masana’antunsu a cikin gida, da kuma sauya manyan hafsoshin soja da suka dade a kan madafun iko. Sai dai wasu na sukar yadda gwamnatin ke murkushe ‘yan adawa da kuma jinkirin mayar da mulki ga farar hula.

Mamady Doumbouya na da aure da wata ‘yar Faransa mai suna Lauriane Doumbouya wacce ke aiki a hukumar ‘yan sandan Faransa (Gendarmerie). Sun haifi yara biyar tare.

Yanzu haka Doumbouya na ci gaba da jagorantar kasar Guinea a matsayin shugaban rikon kwarya, yana kokarin daidaita gyaran tsarin mulki da kuma fuskantar suka daga gida da waje kan tsawaita mulkin soja.

Follow Us