Yadda Kamfanin Jiragen Sama na United Nigeria ya Kwashe Shekaru Huɗu Ba Tare da Samun Tangarda ba

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes27032025_195143_United_Nigeria_ERJ_145_Airborne.jpg


Daga Muhammad Danjuma 
@ Katsina times 

Tun daga watan Fabrairu na shekarar 2021 da kamfanin sufirin jiragen sama na United Nigeria Airlines ya fara aiki, ya kafa tarihi na rashin samun tangarda a dukkanin zirga-zirgarsa.

Mahukunta a bangaren sufurin jiragen sama sun tabbatar da cewa har ya-zuwa yau, ba a taba dakatar da kamfanin ba, ko a sanya masa takunkumi saboda karya ka'idojin sufuri ko na tsaro, duk da cewa yana zirga-zirga a manyan biranen Najeriya goma sha uku.

United Nigeria Airlines na jigilar matafiya tsakanin manyan birane a kullum, biranen sune Abuja, Lagos, Port Harcourt, Enugu, Asaba, Owerri, Yenagoa, Osubi, Anambra, Kano, Sokoto, Benin da Katsina.

Mahukunta a bangaren sufurin jiragen sama sun yaba ma kamfanin bisa kiyaye ka’idojin sufuri da na tsaro da tsaro, wanda hakan ya sa ya samu amincewar fasinjojin jirgin sama a fadin kasar nan.

Kamfanin jirgin saman na United Nigeria Airlines wanda aka yi ma rajista a ƙarƙashin Dokar Kamfanoni masu zaman kansu na shekarar 1990 a Hukumar Kula da Kamfanoni, har ila yau mamba ne na Ƙungiyar Sufurin Jiragen Sama ta Duniya (IATA).

Wani dan kasuwa, dan asalin jihar Anambra Amma haifaffen garin Gombe, Farfesa Obiora Okonkwo, OFR, shi ya kafa kamfanin.

Kamfanin wanda ya fara aiki da jirage hudu, a yau ya bunkasa ya kara yawan jiragensa, ciki har da makeken jirgi kirar Airbus, Embaer 190.

Har ila yau kamfanin na da kwararrun ma'aikata da Suka samu horo da shedar kwarewa daga manyan hukumomi a bangaren sufurin jiragen sama kuma kamfanin na bayar da muhimmanci kwarai ga kiyaye ka'idojin sufurin jirgin sama.

Follow Us