Kungiyoyin Asirin Da Ke Juya Duniya (III)

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes17032025_135232_FB_IMG_1742219414963.jpg

Daga Danjuma Katsina
Mujallar Matasa: Shekarar 2009 - 2010

Skull and Bones

An kafa kungiyar Skull and Bones a shekarar 1832 a Amurka, inda take da cibiyarta a wani gini da aka fi sani da Hubbare. Mafi yawan membobinta ‘yan asalin Amurka ne, kuma daga cikinsu akwai shugabannin kasar da dama. Akwai shugabanni goma na Amurka da suka fito daga wannan kungiya, ciki har da tsohon shugaban kasa George W. Bush. Har ma an taba rawaito Bush yana bayyana wa ‘yan jarida cewa shi dan kungiyar Skull & Bones ne.

The Bohemian Grove

Cibiyar kungiyar Bohemian Grove tana jihar California, Amurka. Wannan kungiya na da membobi daga cikin manyan ‘yan majalisar dokokin Amurka, shahararrun ‘yan jarida, da masu rike da manyan kafafen yada labarai.

The Round Table

Wannan kungiya ta samo asali daga Birtaniya, kuma ta kasance tana kokarin fadada tasirin turawa a kudancin Afirka. Ta taka muhimmiyar rawa wajen kafuwar tsarin mulkin mallaka a yankin, amma bayan da zamanin mulkin mallaka ya kare, sai ta canza hanyoyin aikinta. Yawancin darektocin hukumar leken asiri ta Amurka (CIA) tun daga lokacin kafa ta har zuwa yau, an ce suna daga cikin membobin wannan kungiya.

Ana zargin cewa duk wanda ya yi rashin sa’a aka gayyace shi zuwa wannan kungiya, yana da zabi guda biyu—ya shiga cikinsu, ko kuma ya rasa ransa.

The Inquiry

An kafa wannan kungiya a shekarar 1915, karkashin jagorancin wani soja kuma marubuci, Kanar Edward Mandell House. Mandell House ya rubuta wani littafi mai suna Philip The Administration, wanda ya bayyana manufofin kungiyar. Wannan kungiya ta hada sojoji da masana don tsara dabarun tafiyar da harkokin duniya, musamman a fannin tattalin arziki da siyasa.

Kungiyoyin Asiri a Afirka

Ana zargin cewa akwai shugabannin kasashen Afirka da dama da suka kasance membobin irin wadannan kungiyoyi. Daga cikin sunayen da ake ambato akwai:

John Kufuor (Tsohon Shugaban Ghana)

Jerry J. Rawlings (Tsohon Shugaban Ghana)

Omar Bongo (Tsohon Shugaban Gabon)

Paul Biya (Shugaban Kamaru)

Blaise Compaoré (Tsohon Shugaban Burkina Faso)

Denis Sassou Nguesso (Shugaban Congo-Brazzaville)

Mamadou Tandja (Tsohon Shugaban Nijar)

Louis Botha (Janar na Sojojin Afirka ta Kudu)

Pascal Lissouba (Tsohon Shugaban Congo-Brazzaville)

Idriss Déby (Tsohon Shugaban Chadi)

Robert Guéi (Tsohon Shugaban Sojin Ivory Coast)

Kofi Annan (Tsohon Sakataren Majalisar Dinkin Duniya)

Nelson Mandela (Tsohon Shugaban Afirka ta Kudu) – An ce ya shiga bangaren Black Obedience of American Freemasonry, wanda ake kira Prince Hall.

Wadannan kungiyoyin na ci gaba da taka rawa a siyasar duniya, musamman a fannin tattalin arziki, mulki, da tsarin zamantakewa.

Follow Us