Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya rantsar da Yakubu Sani Haidara, a matsayin sabon Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Jihar, tare da sabbin manyan sakatarori 12.
Bikin rantsar da sabon shugaban ma’aikata da manyan sakatarorin ya gudana ne a ranar Alhamis a tsohon ɗakin taro na gidan gwamnati da ke Gusau.
A cikin Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa, an kuma kafa ofishin mai kula da ayyukan bada tallafi daga waje a ƙarƙashin ofishin gwamna.
Sanarwar ta ƙara da cewa, sabon ofishin da aka kafa zai kasance ƙarƙashin Babban Sakatare, wanda zai kai rahoto ga gwamnan kai tsaye. "Rawar da Babban Sakataren zai taka shi ne daidaita dukkan ayyukan sa da abokan tarayya da shirye-shirye na masu bada tallafi, tare da aiwatar da ayyukan hukumomin gwamnati."
A jawabinsa a wurin rantsarwar, Gwamna Lawal ya yi tsokaci kan sabon shugaban ma’aikatan da aka naɗa a matsayin fitaccen ma’aikacin gwamnati wanda ya yi fice wajen gudanar da ayyukansa na tsawon shekaru talatin.
“An yi maka wannan naɗin ne saboda sadaukarwar ka ga aikin gwamnati. Wannan sabon matsayi zai ba ka damar amfani da ƙwarewar ka wajen sake inganta ma'aikatan gwamnati, haɓaka aiki, da gudanar da aiki cikin ƙwarewa.
“A matsayinka na Shugaban Ma’aikata, kai ne ke da alhakin tafiyar da sauye-sauyen ayyukan gwamnati da wannan gwamnatin ta fara a halin yanzu. Waɗannan sauye-sauyen na da nufin gina ingantaccen tsari wanda zai iya biyan buƙatu da muradin al’ummar jihar Zamfara.
"An ba ka amanar kula da manyan sakatarori da ma'aikatan gwamnati don tabbatar da cewa an tsara manufofi da shirye-shiryen gwamnati yadda ya kamata."
Gwamnan ya kuma bayyana cewa an naɗa Manyan Sakatarorin ne ta hanyar bin tsari da gaskiya. Wannan ya haɗa da kwas mai ƙarfi, rubutaccen jarrabawa, tambayoyin baka, da gwaje-gwaje na tushen ICT, wanda ya ƙare a cikin ƙwarewa a Cibiyar Kula da Ayyukan Jama'a ta Nijeriya (PSIN).
“An sauya fasalin tsarin naɗin Manyan Sakatarori a jihar ne don zaƙulo waɗanda suka dace, wanda aka sanar da mu don tabbatar da cancanta maimakon son kai da son zuciya don ci gaban aiki a ma’aikatun gwamnati.
"Mun yi imanin cewa sake fasalin ma'aikatan gwamnati, wanda shi ne cibiyar tsara manufofi da aiwatar da gwamnati, dole a nemo ƙwararru. Alhamdulillah, da wannan mun kafa tsarin da ya dace kuma wanda zai ɗore, In sha Allahu.
“Bayan an rantsar da ku a matsayin Manyan Sakatarori na Gwamnatin Jihar Zamfara, ya kamata ku fahimci cewa ayyukanku na da matuƙar muhimmanci wajen samun nasarar aiwatar da manufofin gwamnatinmu; Na yi imani da cewa ta hanyar basirarku da kuma iyawar ku, za ku tashi tsaye wajen gudanar ayyukanku cikin himma
“A matsayinku na jami’ai a ma’aikatu, ana sa ran ku daidaita ayyukanku da ajanda shida na wannan gwamnati tare da tabbatar da cewa duk wata manufa da tsare-tsaren da ke ƙarƙashin ku za su tabbatar da manufofinmu huɗu na isar da kyakkyawan shugabanci ga al’ummar Jihar Zamfara.”