Mazauna kauyukan Wagini, Bakon Zabo, da Gimi a kananan hukumomin Batsari da Safana sun yabawa kokarin Gwamna Malam Dikko Umar Radda wajen magance matsalolin tsaro a yankunansu.
A ranar Juma’a, 7 ga Maris, 2025, tawagar ‘yan jarida sun ziyarci yankunan domin tantance halin tsaro da jin ta bakin mazauna kan kalubalen da suka fuskanta.
Mazauna sun bayyana cewa sama da shekara guda kenan ba su fuskanci barazanar tsaro ko hare-haren ‘yan bindiga ba, lamarin da ya sauya rayuwarsu.
A baya, manoma da ke noma irin su rogo, dankali, masara, gero, da dawa sun fuskanci cikas wajen shiga gonakinsu saboda tsoron hare-haren ‘yan ta’adda, wanda ya shafi tattalin arzikin yankin.
Sai dai yanzu, mazauna sun tabbatar da samun sauyi a harkar tsaro, wanda suka danganta da matakan da gwamnan ke dauka wajen yaki da ‘yan ta’adda.
Daga karshe, sun nuna godiyarsu tare da yin alkawarin mara wa gwamnati baya wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin jihar.