Katsina Times | Abuja, 19 ga Fabrairu, 2025
Hukumar Raya Kasashen Afrika AUDA-NEPAD a Nigeriya ta gudanar da taro na musamman tare da masu kula da shirin a matakin jiha da kuma Kwamishinonin Noma daga jihohi guda bakwai da aka zaba domin tabbatar da dorewar Shirin Tallafa wa Kananan Manoma.
Taron tattaunawar ya mayar da hankali kan inganta wadatar abinci, bunkasa rayuwar jama’a a karkara, da tabbatar da aiwatar da shirin cikin inganci. Shugaban AUDA-NEPAD a Nigeriya, Alhaji Jabiru Salisu Abdullahi, ya jaddada aniyar hukumar wajen tabbatar da tsari mai inganci na sa ido domin tabbatar da gaskiya da kuma ingantaccen sakamako, don haka tabbatar da dacewar tallafin da AUDA-NEPAD Continental ta samar domin aiwatar da shirin.
Muhimman batutuwan da aka tattauna sun hada da rawar da jihohi ke takawa, sabbin hanyoyin warware matsaloli, da kuma hadin gwiwa don magance kalubalen da ke fuskantar Kananan manoma.
A karshe, mahalarta taron sun kuduri aniyar tabbatar da nasarar shirin, domin ya zama ginshiki wajen sauya fasalin noma da bunkasa tattalin arzikin Najeriya.