Mun Karbi Kaddara Zamu Yi Kokari a Zabe Mai Zuwa. .... Inji Inter-party advisory council( IPAC)

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes16022025_162748_IMG-20250216-WA0054.jpg

Muhammad Ali Hafizy, Katsina Times.


A wani taron manena da gamayyar kungiyar jam'iyu ta kira a ranar Lahadi 16 ga watan Fabrairu 2025, a shelkwatar ta dake kofar durbi cikin garin Katsina.

Shugaban kungiyar, Alhaji Salimu Lawal Boyi, ya mika ga jinjinar shi ga Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Katsina, bisa namijin kokari da tayi wajen ganin an gabatar da muhimmin zaben ciyamomi da kansiloli a fadin jihar ba tare da samun wata hayaniya ba ko tashin hankali.

Sannan ya yi jinjina ga dukkan yan takarkarun da suka fito zaben amma basu samu nasara ba, yayi jinjina a gare su tare da karfafa masu gwiwa akan kara dagewa a zabe mai zuwa.

Haka zalika, Boyi yayi kira ga yan takarkarun da cewa kada wannan rashin nasarar da suka yi ta zama ta sanyaya masu gwiwa a nan gaba, yayi kira gare su da su koma baya su jajirce su kara shiri zuwa zabe mai zuwa.

Daga karshe ya taya wadanda suka samu nasara murna tare da karbar ƙaddara ga wadanda basu samu nasara ba.

Follow Us