Yusuf Abubakar Nabukka
10/02/2025
Matasa na da rawar da za su taka a siyasa, amma dole ne su yi tunani mai zurfi game da tasirin wannan rawa a rayuwarsu. Yayin da ake fama da matsaloli kamar rashin lafiya, yunwa, da rashin tsaro, ya kamata matasa su fahimci cewa siyasa ba ta cancanci sadaukar da rayuwarsu a banza ba.
Duk wanda ke bayar da kuɗi don a mara masa baya a siyasa, abu mafi muhimmanci da ya kamata ya ba ku shine ilimi, sana’a, da hanyoyin da za su inganta rayuwarku. Ku tambayi kanku: shin waɗanda kuke aiki a gare su suna cikin wahala irin taku? Bayan zaɓe, su da iyalansu suna cikin jin daɗi, amma ku kuna cigaba da fuskantar wahala. Idan da gaske suna ƙaunarku, da sun taimaka muku tun tuni.
Matasa dole su farka! Bai kamata a cutar da juna saboda son zuciya da siyasa ba. Maimakon haka, ku mai da hankali kan sana’a, ilimi, da abubuwan da za su amfanar da ku a nan gaba. Canjin da ake nema ba zai zo ta hanyar tashin hankali ba, sai dai ta hanyar hakuri, aiki tukuru, da neman mafita mai dorewa.
A matsayinku na matasan Najeriya, ya kamata ku fahimci nauyin da ke kanku wajen gina kyakkyawar makoma. Kada soyayya ko biyayya ga wani su jefa ku cikin halaka. Ku zama matasa masu wayo, ku kauce wa rikici, ku yi ƙoƙari ku karanci addini da zamani. Domin a yau, dole ne mutum ya dage sannan ake samun ci gaba da mutunci.
Ku nemi sana’a, ku tashi ku gina makomarku da kanku!