Dawowar Musa Gafai a APC: Gidauniyar Gwagware Ta Sha Alwashin Karfafa Goyon Bayansa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes05022025_224812_FB_IMG_1738795525209.jpg



Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times 

Shugaban Gidauniyar Gwagware, Hon. Yusuf Ali Musawa (Talban Musawa), ya bayyana cewa Hon. Musa Gafai ya taka muhimmiyar rawa a tafiyar Gwamna Dikko Umaru Radda, yana mai jaddada cewa ba za su sake barinsa ya fice daga jam’iyyar APC ba.  

Ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar bakuncin tawagar Dikko Project Movement karkashin jagorancin Hon. Musa Gafai, wadda ta kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa.  

A yayin taron, Hon. Yusuf Ali Musawa ya yi nuni da cewa rashin irin su Musa Gafai a jam’iyyar APC ne ya haddasa asarar sama da kuri’u 30,000 a zaben shugaban kasa a Jihar Katsina. Ya ce, “Duk da muna a kauyuka muna nemowa jam’iyya kuri’u, wasu na birni suna mana illar.”  

Shugaban Gidauniyar Gwagware ya jaddada cewa su na da cikakken goyon bayan Dikko Project Movement duba da irin manufofin kungiyar na taimakon al’umma da wayar da kai kan ayyukan alherin Gwamna Dikko Radda.  

A nasa jawabin, Hon. Musa Gafai ya bayyana cewa sun kawo ziyarar domin neman albarka daga jagoransu, yana mai cewa: “Dukkan abin da mutum zai yi, idan yana neman albarka, ya fara nema daga gida.”  

Ya kuma bukaci shugaba Yusuf Ali Musawa da ya sanya hannu wajen tallafa musu da shawarwari domin samun damar kaiwa ga matsayoyin da ba za su iya kaiwa ba da kansu, duba da irin kusancinsa da Gwamna Dikko Radda.  

Daga karshe, Hon. Musa Gafai ya mika sakon godiya ga Gwamna Malam Dikko Radda bisa irin mutuntaka da kulawar da yake ba su a kowane lokaci.  

Taron ya samu halartar manyan jiga-jigan kungiyar Dikko Project Movement, ciki har da wasu daga cikin shugabanninta da ‘yan takarar kansiloli, tare da masu rike da mukaman siyasa a halin yanzu.

Follow Us