NYCN Jihar Katsina Ta Gudanar da Taron Inganta Jagorancin Matasa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes02022025_204831_IMG_9662.jpg

NYCN Jihar Katsina Ta Gudanar da Taron Inganta Jagorancin Matasa


Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times

Majalisar Matasa ta Kasa (NYCN), reshen Jihar Katsina, ta gudanar da taron Kwamitin Gudanarwa domin karfafa shugabanci da daidaita tsarin gudanarwa a tsakanin matasa a fadin jihar. Wannan taro na musamman, wanda aka gudanar a ranar Lahadi, 2 ga Fabrairu, 2025, a Babban Dakin Taro na Sakatariyar Karamar Hukumar Katsina (General Shehu Musa Yar’adua House), ya tattaro manyan masu ruwa da tsaki daga kungiyoyin matasa da bangarori daban-daban na majalisar.

A karkashin jagorancin Shugaban NYCN Jihar Katsina, Comrade Shamsudden Ibrahim Shamo, taron ya samu halartar mambobin kwamitin zartarwa na jiha, mambobin kwamitin gudanarwa, mambobin kwamitin kulawa, mambobin kwamitin shawara, shugabannin kungiyoyin matasa masu zaman kansu (VYOs), da shugabannin rassan NYCN na kananan hukumomi.

A jawabinsa, Comrade Shamo ya bayyana godiyarsa ga dukkan mahalarta taron tare da jaddada bukatar hadin kai a tsakanin shugabannin matasa domin magance kalubalen da ke fuskantar matasa a jihar Katsina. Ya tabbatar da cewa NYCN za ta ci gaba da aiwatar da tsare-tsare da manufofin bunkasa matasa da karfafa basirarsu, yana mai cewa:

"Wannan taro yana da matukar muhimmanci domin ƙarfafa tsarin shugabancin matasa da tabbatar da cewa muna tafiya a turbar da ta dace don inganta rayuwar matasan jihar Katsina."

Comrade Shamo ya yi bayani kan yadda NYCN ta samu ci gaba a shekarun da suka gabata duk da matsalolin da aka fuskanta. Ya jaddada cewa tare da hadin gwiwa, majalisar ta samu nasarar shirya da gudanar da zabuka cikin kankanin lokaci, wanda ya tabbatar da ingantacciyar tafiya ta shugabanci.

Ya kuma tabo wasu matsalolin da majalisar ke fuskanta, yana mai bayyana cewa akwai wasu da ke kokarin kawo cikas ga tafiyar matasa. Sai dai ya bayyana cewa, tare da hadin kai, NYCN za ta ci gaba da taka rawar gani a matsayin jigon bunkasa matasa da samar da hadin gwiwa da gwamnati domin cigaban jihar.

Shamo Ya Jinjina wa Gwamna Radda

A yayin taron, Comrade Shamo ya bayyana cewa Majalisar Matasa ta Kasa (NYCN) ta taka rawar gani tun kafin Gwamna Malam Dikko Umar Radda ya hau mulki, inda suka bayar da gudunmawa wajen tallafa masa a yakin neman zabensa. Ya ce:

"Mun shiga tafiyar Gwamna Malam Dikko Umar Radda tun kafin ya zama gwamna, kuma mun bada gudunmawa sosai. Haka shi ma ya jinjina mana tare da bayar da tallafi don ci gaba da bunkasa matasa a jihar Katsina."

A kammala taron, an cimma kuduri da dama da za a aiwatar domin kara karfafa matasa da tabbatar da ci gaba mai dorewa. Comrade Shamo ya bukaci shugabannin matasa su ci gaba da hada kai da kungiyoyi masu zaman kansu domin inganta rayuwar matasa da bunkasa ilimi, sana'o’i, da jagoranci a jihar.

NYCN Jihar Katsina na ci gaba da taka rawar gani a matsayin gadar da ke hada gwamnati da matasa, tare da tabbatar da cewa matasa suna da tasiri a tafiyar da shugabanci da ci gaban jihar. Wannan taro ya kara tabbatar da kudirin majalisar na inganta jagoranci, daidaita tsarin gudanarwa, da samar da ci gaba mai dorewa ga matasan Jihar Katsina.

Follow Us