Katsina Times
Hukumar Kula da Ilimin Almajirai da Yara da Ba sa Zuwa Makaranta ta Ƙasa tana farin cikin gayyatar daliban da suka cancanta daga makarantu Tsangaya don shiga cikin shirin horaswa na watanni tara. Wannan shirin yana da nufin ba da horo kan sana'o'in hannu, inganta samun dogaro da kai, da haɓaka jin daɗin rayuwa gaba ɗaya.
Ka'idojin Cancanta
Domin cancanta shiga wannan shirin, dalibi dole ya kasance:
1. Dalibi ne da ke karatu a makarantar Tsangaya.
2. Mai haddar Alƙur'ani ne.
3. Yana da shekaru tsakanin 16 zuwa 26.
4. Lafiyar jikinsa tana da inganci da zata ba shi damar halartar zaman horo daga ƙarfe 8 na safe zuwa 6 na yamma.
5. Ya samu amincewar malaminsa da iyayensa.
6. Ba shi da wata matsala da hukumomin tsaro ko kotuna.
Yadda Ake Neman Shiga Shirin
Masu sha'awar shiga shirin za su iya aiko da bukatunsu tare da bayanan sunayensu da lambobin tuntuɓarsu ta:
- Shafin Facebook: [ncaosce.ng](http://www.ncaosce.ng)
-Lamba/WhatsApp: 09064313510 (Sadig)
- Adireshi: No. 2, Zuma Close, Udi Hills, Aso Drive, Asokoro, Abuja.
Ranar Ƙarshe na Neman Shiga
Masu sha'awar shiga shirin su tabbatar sun aika da bukatunsu kafin ranar Alhamis, 30 ga Janairu, 2025.
Wannan dama ce ta musamman ga daliban Tsangaya don samun horo da zai inganta rayuwarsu da kuma ba su damar taimaka wa kansu da al'umma gaba ɗaya.