ANA GUDANAR DA MAKON SHEHU A KANO INDA AKE GABATAR DA MUHIMMAN TAKARDU NA ILIMI
- Sulaiman Umar
- 23 Jan, 2025
- 22
Ranar 18 ga watan Janairu na shekarar 2025 aka fara gagarumin taron makon Shehu Ibrahim Niass na bana wanda qungiyar Maj’mau Ahabab Sheikh Ibrahim Niass ta saba shiryawa duk shekara qarqashin jagorancin shugabanta na qasa , Sheikh Tijjani Sani Auwalu kwamishina na addinai na Kano kuma jika ga Sehi Ibrahim Niass. Ana gabatar da wannan gagarumin mauludi duk shekara don tunawa da rayuwa da ayyukan Shehin Malamin xariqar Tijjaniya wanda ya yi mata hidima Sheikh Ibrahim Inyas. Ana gudanar da Mauludin bana a Kano ne qarqashin shugabancin Halifa Sayyadi Bashir Tijjani Usman Zangon Barebari.
An tsara a taron yadda za a yi kwana bakwai ana yinsa sannan kullum za a gabatar da takardu guda uku a rufaffen xakin taro na masallacin Shehu Tijjani da ke Qofar mata, Kano. Rana ta farko an buxe taron makon Shehu a Kano ranar 18 ga wata inda mataimakin gwamnan jihar Kano Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo ya halarta tare da jagoranci qaddamar da taron. Sai zama na rana wanda Barista Habibu Xan Almajiri ya gabatar . Sheikh Al-Sharif Ibrahim Tahir ya gabatar da takarda mai suna “Sanin siyasa a wajen Sheikh Ibrahim Inyas”. Wannan maudu’i ya tavo sanin siyasa a addinin Musulunci da sanin siyasa na duniya da sanin mu’amala da zamantakewa, da ba wa kowa haqqinsa kamar yadda ya dace a inda ya dace. Wannan maudu’i ne mai faxin gaske wanda aka yi masa kyakkyawan nazari aka warware zare da abawa. Khalifa Aliyu Sulaiman Kila ya yi masa ta’aliki mai faxi da gamsarwa. A zaman yamma kuwa an tattauna kan “Sheikh Muhammad Salga jagoran makarantar fiqhu na malikiyya” wanda Sheikh Abdullahi Uwais Limanci ya gabatar. Mai gabatar da takardar ya kawo tarihi da gwagwarmayar karatu da karantarwar Sheikh Muhammadu Salga da yadda ya zama fitaccen masani akan fiqhu Malikiyya a Afrika ba a iya Nijeriya kaxai ba. Wanda Sheikh Ibrahim Shehu Maihula ya yi ta’aliqi da qarin haske. Bayan an kammala Dr Sunusi Muhammad Qani ya yi jawabin godiya. A zaman safiya a rana ta biyu Sheikh Muniru Adamu Koza ya gabatar da takarda mai suna “Rawar da Shehu ya taka wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali” a muhadarar Malamin ya nuna muhimmancin zaman lafiya da yadda Shehu Ibrahim ya yi kira da zaman lafiya da cire kowanne savani da tsayawa kan musulmi duka xan uwan musulmi ne don haka a qaunaci juna da zauna da juna lafiya. Wanda ya yi ta’aliqi a wannan muhadara shi ne Sheikh Abubakar Maxatai. Sheikh Maxatai ya yi qarin haske kan maudu’in da Sheikh Koza ya yi tare da qarin bayani mai gamsarwa kan muhimmancin zaman lafiya a wannan zamanin da cigaban da yake kawowa al’umma. A rana ta biyun da yamma an babatar da takarda mai suna “Hanyar koyarwa da jagoranci ta Sheikh Muhammadu Al-Thani Hassan Kafinga” wanda Dr Umar Muhammad Kani inda Malam Sa’id Baqin Ruwa ya yi masa ta’aliqi. Rana ta uku Barista Habibu Xan Almajiri ya gabatar da takarda mai suna “Alaqar Shehu Ibrahim Inyas da addinin Musulunci” Wannan takardar ta yi dogon nazari kan yadda Shehu Ibrahim ya yi hidima ga addinin Musulunci ba a iya Afrika a duniya gabaki xaya da yadda ya xora dukkan al’amuransa kan kitabu wassunna kuma irin koyarwar da duk mai da’awar Xariqa da Faila ya kamata ya yi kenan don koyi da Shehu Ibrahim Niass. Iman ya fito da alaqar Sheikh Ibrahim da ilimin addinin Musulunci kwarai da gaske , inda Gwani Dr. Yusuf Ishaq Rabi’u ya yi masa taliqi. Sai zaman rana a rana ta uku an gabatar da takarda mai suna “Bita akan Littattafan Afrika ga ‘yan Afrika” wadda Dr Atiku Balarabe Gusau ya gabatar sanna Dr Lawi Sheikh Atiku Sanka ya yi wa kyakkyawa kuma gamsasshen ta’aliqi. Zaman yamma na rana ta uku, Dr Tahir Lawan Mu’azu ne ya gabatar da takarda akan “Tarihi da ayyukan Sheikh Atiku Sanka” Marubucin ya yi kyakkyawan jawabi filla-filla kan rayuwa da gwagwarmaya da ayyukan Shehu Atiku Sanka. Manazarcin ya yi zurfaffen bincike kan wannan maudu’i. Bayan Dr Tahir Lawan Mu’azu ya gabatar da takardar sai Imam Nazifi Gambo ya yi masa ta’aliqi. A rana ta huxu za a gabatar da takarda mai suna “Hanyar da Sheikh Ibrahim Inyas ya bi yayin kira ga Allah” wanda Dr Mustapha Kagarko zai gabatar sai kuma Imam Xayyib Muhammad Xan Almajiri zai yi ta’aliqi. Rana ta biyu da rana Dr Saminu Xalhatu Gusau zai gabatar da takarda inda Sheikh Mustapha Maijama’a zai yi ta’aliqi. Za a tattauna za su tattauna akan “Tajdidi a manhajar Sheikh Ibrahim Niass”. Zaman yamma za a tattauna akan “Rayuwa da ayyukan Shehu Usman Maihula” Wanda zai gabatar da Muhadara shi ne Dr Ibrahim Auwal Ibrahim inda Dr Mustapha Tijjani zai yi masa ta’aliqi. Rana ta biyar Iman Dr Muhammad Nazifi Bichi zai gabatar da takardarsa mai suna “Kwarewar Shehu Ibrahim Inyas a harshen Larabci: Tsince-tsince a Diwani” inda Malam Zubairu Madigawa zai yi ta’aliqi. Zaman rana Farfesa Muhammad Haruna Haxeja shi zai gabatar da takarda inda Malam Ahmad Tijjani Mai Salati Indabawa zai yi ta’aliqi. Maudu’in da za a tattauna shi ne “Sheikh Ibrahim da yadda yake tu’ammali da shari’ar musulunci” Makon Shehu Rana ta shida Farfesa Abubakar Abubakar Yagawal ne zai fara gabatar da takarda da safe zai gabatar da takarda mai suna “Fahimta game da tafarkin Tijjaniya tsakanin Haqiqa da tunanin mutane” wanda Sheikh Muhammad Abdullahi Suru zai yi masa ta’alaqa sai kuma zama na rana wanda Dr Nasidi Abubakar zai gabatar da takarda mai suna “Shawarwarin Sheikh Ibrahim Niass ga mabiya game da qarfafa qauna a cikin Allah” inda Dr Abdullahi Mahmud Salga zai yi ta’aliqi. Sai kuma zaman yamma, inda Dr Aminu Sufi zai gabatar da takarda inda Injiniya Ali Sani Maihula zai yi ta’aliqi. Za a rufe taron ranar juma’a 24 ga watan Janairu 2025 inda asabar za a wayi gari da taron Mauludi na Shehu Ibrahim Inyas.
Haqiqa wannan mako na Sheikh Ibrahim Niass yana xauke darussa daban-daban na tarihi da gwagwarmayar malamai na xariqar Tijjaniya da Failar Shehu Ibrahim tun daga kan Shehu Ibrahim da kuma almajiransa kan yaxa addinin Musulunci da yaxa ilimi na shari’a kamar fiqhu da ilimi na lugga da zamantakewa da qaunar juna da muhimmancin zaman lafiya don cigaban qasa da al’umma. Shehunnan xariqa sun yi ayyuka da dama inda wasu an san qoqarin da suka yi ana kuma fito da qoqarin nasu ne kawai a irin wannan zama , inda kuma wasu sai a irin wannan zama ne ake gane hidimar da suka yi wa addinin Musulunci. Makon Shehu da ake gabatarwa zai qara samar da haxin kan al’ummar Musulmi musamman ‘yan xariqar Tijjaniya da failar Shehu. Dubban jama’a ne suke halartar wannan zama na makon Shehu don jin karatuka da wayar da kai da bayar da ilimi da manyan malamai ke yi kullum. Daga cikin jagororin wannan makon Shehu akwai Sheikh Ibrahim Shehi Maihula (Shehi Shehi) da Halifan Shehu Maihula Sheikh Sani Shehu Maihula shugaban majalisar Shura ta xariqar Tijjaniya. Sai Dr. Lawi Atiku Sanka da Khalifa Sheikh Tuhami Sanka da Sayyadi Sheikh Bashir Usman Zangon Barebari da Sheikh Halifa Sukairaju Salga da da Halifa Kafinga Dr. Sunusi Qani da Barista Habibu Xan Almajiri da shugaban kwamitin yaxa labarai Dr Aliyu Tamasi.