Dan Takarar Shugaban Karamar Hukuma Na APC Ya Tallafawa Daliban Firamare a Katsina

top-news

Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times, 22 ga Janairu, 2025

A wani yunkuri na bunkasa ilimi da rage radadin rayuwa ga yara, dan takarar shugabancin karamar hukumar Katsina a karkashin jam'iyyar APC, Malam Isah Miqdad AD Saude, ya kaddamar da wani shirin tallafawa daliban firamare. 

Da yake jawabi yayin taron da aka gudanar a Kambarawa, kusa da Filin Jirgin Sama na Umaru Musa Yar’adua, Malam Isah ya fayyace cewa wannan shiri ba ya da wata manufa ta siyasa. Ya ce, "Mun shirya wannan domin tallafawa yara. Idan akwai wanda yake ganin siyasa ce, su sani cewa wadannan yaran ma ba su kai shekarun yin zabe ba." Ya bayyana cewa gudunmawar ta samu ne daga goyon bayan wasu fitattun mutane a Katsina. 

Da yake bayani kan dalilin shirin, Isah ya ce, "A cikin kwamitinmu na ilimi, mun fahimci cewa akwai bukatar samar da wata hanya da za ta inganta harkar ilimi tare da rage wahalhalun da iyaye suke fuskanta." Ya kuma yi kira ga al’umma da su hada kai domin cigaban ilimi, yana mai cewa ilimi shi ne ginshiƙin ci gaban al’umma.

Dan takarar ya kuma nuna godiya ga fitattun mutane da kungiyoyi da suka bayar da gudunmawa ga tafiyar sa, ciki har da Alhaji Ido Kwado (Sarkin Aiki), Alhaji Musa Gafai, Alhaji Dahiru Danmarna, Alhaji Lolo Dakare da kuma Hon. Ali Abu Albaba.

Shugaban Kwamitin Ilimi, Malam Isma’il Tukur, ya bayyana yadda aka tsara shirin. Ya ce an tallafawa daliban firamare 1,000 daga makarantu 24 a dukkan mazabun karamar hukumar Katsina guda 12. An basu littattafai, kayan makaranta, da kudaden sufuri. Haka kuma, an rarraba akwatunan taimakon gaggawa (First Aid Box) ga kowane makaranta.

A matakin sakandare kuwa, an bayar da tallafin karatu ga dalibai 48 wanda zai dauki nauyin karatunsu har zuwa kammalawa a shirin farko. Baya ga haka, dalibai 222 daga makarantu na Community School sun amfana da kayan karatu da tallafin sufuri.

Shugaban Hukumar Tallafin Karatu ta Jihar Katsina, Dr. Aminu Yusuf Tsauri, ya yabawa shirin, yana mai kwatanta shi da hangen nesan Gwamna Dikko Umar Radda. Ya kuma bayyana cewa hukumar ta ware makudan kudade domin tallafawa dalibai, har da tura wasu zuwa kasashen waje domin karatu.

Haka zalika, dan majalisar dokokin jihar Katsina, Hon. Ali Abu Albaba, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su shiga cikin harkar tallafawa ilimi. Fitaccen dan siyasar Katsina, Alhaji Ido Kwado, ya tabbatar da goyon bayansa ga wannan shiri, yana mai bayyana shi a matsayin wata babbar dama ga al’umma.

Kungiyoyi kamar su Dikko Project, Lamido Foundation, da Gwagware Foundation sun bayar da tallafi domin kara wa shirin kuzari tare da saukaka zirga-zirgar dalibai.

Taron ya kasance kashi na uku cikin shirye-shiryen tallafin ilimi da Isah ya gudanar, wanda ya kara tabbatar da jajircewarsa wajen gina al’umma mai ilimi a karamar hukumar Katsina.