SABUWAR RONI A HANNUN DR. ABBA YA'U
- Katsina City News
- 07 Jan, 2025
- 122
Daga Yusuf Kabir
kabiruyusuf533@gmail.com
09063281016.
Garin Roni gari ne mai daɗaɗɗen Tarihi tun dauri.Yana cikin ƙananan Hukumomin Jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya.Garin tun daga dawowar Dimokuraɗiyya ya sami shuwagabanni a matakin ƙaramar Hukuma da dama,amma ba a taɓa samun shugaban ƙaramar hukumar da ya bayar da gudummawa ga al'ummar da yake mulka ba kamar Dr.Abba YA'U RONI.Duk da watanni ya yi a kan karagar mulki,amma ya yi ayyuka daban-daban da za a yi iya tsammanin ya yi shekara da shekaru ne.Ga waɗansu daga cikin ayyukansa da muka tsakurowa mai karatu:-
1.A ranar 1/1/2/2025 ƘADDAMAR DA 'DEGREE AND PGDE PROGRAMME IN EDUCATION' A CIKIN GARIN RONI.
Babban burin Dr. Abba YA'U,B bunƙasa harkokin rayuwar al'ummar ta ɓangaren daban-daban domin ganin an inganta rayuwar matasa da masu kishin yin karatu kuma mu ba su ƙwarin gwiwar domin cikar maradun su na rayuwarsu.
A ranar Dr.Ya yi alƙawarin zai bayar da gudumuwa da bada 'schoolship' kyauta ga ɗalibai matasa masu niyyar yin karatu kuma duk abinda ake buƙata zai ci gaba tallafawa ɗalibai domin kara basu ƙwarin gwiwar
gudunar da karatun nasu cikin kwanciyar hankali da nutsuwa.
Taron ya samun hallartar manya ɓaki na gida da wajen wanda mai girma Alhaji Nasir sani jakaraɗan kazaure Hakimin Amaryawa kuma wakilin Roni sai Alhaji Ibrahim Dahiru uban taro mallam salisu Hayyo Malam Kabiru Abdullahi da sauran manya ɓaki.Wannan ba a taɓa kawo ci gaban hakan ba sai a yanzu.
2..ROUND ABOUT (SHA-TALE-TALE) A KARAMAR HUKUMAR RONI KANHAWA
A ranar Juma'a 3/1/2025 Shugaban karamar hukumar Roni Hon Dr Abba Ya'u ya aiko injiniyoyi domin su duba gurin da zai gudanar da babban shataletale (Round About) a Kanhawa domin ci gaban al'atummar ƙaramar Hukumar Roni,da kuma kaucewa yawan faruwar haɗarurruka a faɗin ƙaramar Hukumar ta Roni.
2.GINA KASUWAR DAGEJI DOMIN BUNƘASA TATTALIN ARZIƘI
A ranar 24/12/2024 ne wata tawaga a ƙarƙashin Dr.Abba Ya'u suka ziyarci kasuwar Dageji domin ƙoƙarin bunƙasa harkokin cinikayya da yau kullum wanda za a sami hanyoyin samun ƙuɗaɗen shiga cikin wƙaramar hukumar shi ya sa ya yi tsari mai kyau na ɗaga darajar kasuwar domin mayar da ita ta zamanin wanda yanzu haka tsare-tsaren sun yi nisa na bunƙasa ta.
3.ƁANGAREN INGANTA HARKAR NOMA DOMIN BUNƘASA HARKOKIN RAYUWAR AL'UMMAR DR YA ZIYARAR CI WASU GONAKIN NOMAN RANI DAKE CIKIN MAZAƁAR GORA
4.A ranar 23/12/2024 ne dai Dr.Abba Ya'u bisa doron ƙudurin sa wanda yake a ransa, noma yana ɗaya daga cikin hanyoyin da yake ganin zai samar da ci gaba. domin ko da yaushe ƙoƙarin sa shi ne ɓullo da wasu sabbin tsare-tsare kan noma rani dana damuna wanda za'a koya wa matasa noma zamani kuma da sabbin hanyoyin zamani.
Maigirma Hon Dr Abba Ya'u Roni zaɓaɓɓen shugaban karamar Hukumar tare da mataimakin sa Hon.Bello Mohd Amaryawa, sun ziyarar ci wasu daga gonakin noman rani wanda suke cikin Mazaɓar gora domin ganin yadda yanayin gonakin da kuma yadda za'a kawo hanyoyin samun ayyukan ci gaban cikin wannan gonakin domin matasa da al'umma su amfana.
5.HON DR ABBA YAU RONI YA KAMMALA AIKIN GYARAN SOLAR RUWAN A GARURUWAN GANGARE,ZUGAI AN KAWO SABBIN PENEL DA KEBEL DOMIN MAGANCE MATSALAR RUWAN SHA
Matsalar Ruwan sha na cikin wacce ta ke damun al'ummar ƙaramar Hukumar Toni,hakan ya sa a cikin burisa shine daƙile matsalolin rashin ruwan sha da ke damun wasu mazabun dake cikin faɗin ƙaramar Hukumar Roni baki ɗaya.
6. A ranar 18/12/2024 Dr.Abba YA'U ka karɓi AWARD na karramawa daga 'Bandirawo Fulbe Youth Association Of Nigeria, Jigawa State Chapter.Wannan ya
7.KAMMALA GYARAN HANYAR MATSIGA ZUWA TSUBUT.
A ranar 18/12/2024
Shugaban ƙaramar Hukumar hukumar Roni Hon Dr Abba Ya'u Roni ya kanmyala gyaran hanyar matsiga zuwa tsubut domin mutanan yankin su ci gaba da gudanar da tafiye-tafiyen su cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.
8.FARFAƊO DA GIDAN RUWA A KARAMAR HUKUMAR RONI.
A Ranar 16/12/2024 dai Dr.Abba Ya'u ya farfaɗo da gidan ruwan karamar hukumar Roni domin magance matsalar Ruwan sha da ke addabar al'umma.
9.A ranar 8/12/2024 ZAƁAƁƁEN SHUGABAN ƘARAMAR HUKUMAR RONI HON DR ABBA YA'U YA ZIYARCI BABBAN LIKITA DA YAKE DUBA MARASA LAFIYA A KARAMAR HUKUMAR Wannan kuma yana cikin damuwarsa a kan lafiyar al'umma.
Ziyarar dai da ta gudana a ranar 08/12/2024 mai girma shugaban ƙaramar Hukumar hukumar Roni Hon Dr Abba Ya'u ya ziyarci babban likita da yake duba marasa lafiya domin tattauna muhimman abubuwan da suka danganci harkar lafiya a karamar hukumar Roni domin inganta ɓangaren lafiya,kuma in da ya ƙarawa babban likitan kuɗi akan yadda ake biyan sa a baya, ddomin kawo ci gaba a ɓangaren lafiya.
10.A ranar 6/12/2024 ZIYARA TA MUSAMMANI GA WAƊANDA SUKA TAFI NEMAN AIKIN SOJA.
A ranar 06/12/2024 mai girma zaɓaɓɓen Shugaban ƙaramar Hukumar hukumar Roni Hon Dr Abba Ya'u ya kai wa wanda suka tafi neman aikin soja a sansanin ɗaukar horo na sojan ƙasa da ke Dutse babban birnin jihar jigawa.Shugaban iya gwangwaje su da tagomashin alkairi idan ya sayawa kowa kayan ɗaukar horo tun taga riga, wando, takalmi,da kuma safa, kuma sun fito sun nuna jin daɗinsu ga mai girma shugaban ƙaramar Hukumar Roni Hon Dr Abba Ya'u da Hon Ismaila Dahiru SSA Youths.
11. GININ BABBAN ƊAKIN TARO
Dr Abba Ya'u bisa kishinsa ya ɗauki nauyin gina babban ɗakin taro ga al'ummar ƙaramar Hukumar Roni.
12.AIKIN GYARAN OFISHIN JAMI'AN CIVIL DEFENCE OUT POST
A ranar 30/11/2024,Dr Abba Ya'u tare da
Hon Lawan Tambari Ɗansure Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jahar jigawa suka ziyarci ofishin jami'an tsaron jar kwala (NCDC) domin ganin yadda aikin gyaran Ofishin yake gudanuwa.
13. ZIYARAR 'YAN SANDA DA SUKE TRAINING A KADUNA.
A Ranar 27/11/2024 ne dai Shugaban ƙaramar Hukumar Roni hon Dr Abba Ya'u ya ziyarci asalin matasan dake ƙaramar Hukumar Roni wanda suke training a makarantar koyon aikin ɗan sanda a cida ke garin Kaduna domin ganin yadda training ɗin su yake gudanuwa.
14.DAUKAR NAUYIN ƊALIBAI A MAKARANTAR KOYON AIKIN JIYA DA HAIHUWA TA LAFIYA DAKE BIRNIN KUDU JIHAR JIGAWA.
A ranar 14/11/2024 ne Shugaban ƙaramar Hukumar hukumar Roni Hon.Dr.Abba Ya'u Roni ya ɗauki nauyin ɗaliban da Allah ya bawa nasarar a jarabar da suka zana ta foundation year program (FYP) wanda za ta basu damar karatun koyon aikin haihuwa wacce Jihar Jigawa take ɗauka duk shekara na (FYP) Wato FOUNDATION YEAR PROGRAM.
Waɗannan tsakure ne daga ayyukan ci gaba da Hon.Dr.Abba Ya'u yake aiwatarwa a ƙaramar hukumar Roni da ke jihar Jigawa a cikin ƙasa da shekara ɗaya.
Wani abun farin ciki shi ne,Dr.Abba Ya'u ya kasance wanda yake da Foundation na tallafawa Ɗalibai,marayu da marassa ƙarfi tun kafin ya zamanto shugaban ƙaramar Hukumar Roni.