Gwamnatin Kano ta yi watsi da ƙudirorin dokar haraji
- Katsina City News
- 02 Jan, 2025
- 142
Gwamnatin jihar Kano ta yi watsi da ƙudirorin dokar haraji da ake ta cece-kuce s kan shi tsawon watanni a Nijeriya.
Gwamnatin, ta bakin mataimakin gwamnan, mataimakin gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo, a wajen bikin sabuwar shekara da ya gudana a filin Mahaha a Kano, ta baiyana matsayin ta cewa ba ta tare da waɗannan ƙudirori.
A wata sanarwa da kakakin mataimakin gwamnan, Ibrahim Garba Shuaibu ya fitar, Gwarzo ya ce kudirorin dokar haraji ba shi ne mafita a halin matsin tattalin arziki da ake fama da shi a kasar.
Gwarzl ya kara da cewa gwamnatin jihar ba ta goyon bayan ƙudirorin, inda ya yabawa al'ummar jihar Kano bisa juriya da hakuri da halin kunci rayuwa da ake fama da shi a ƙasar.
Daily Nigeria Hausa