Kano: An Gudanar Da Bikin Kaddamar Da Kwamitin Koli Na Majalisar Malaman Fada A Masarautar Gaya

top-news

Daga Bilkisu Yusuf Ali

A ranar 23/12/2024 a fadar Maimartaba Sarkin Gaya, Alhaji Dr Aliyu Ibrahim (Kirmau Mai gabas) inda Maimartaba Sarki Ya Qaddamar da Kwamitin Koli na Majalisar Malaman Fada(Supreme council of Ulamaa, Gaya Emirate) Karkashin Jagorancin Sarkin Malaman Gaya Mal Munzir Sheikh Dr Yusuf Ali, Majalisar Ta Kunshi Malamai ma banbata Aqida daban daban.


Wanda Shine dama burin Maimartaba Sarki wajan Samar da hadin kai tare da zama Murya daya ga duk Malamin da yake wannan Masarauta Mai albarka. inda Larabawan Masar suka zo shaidawa da Kuma fatan Alheri da bada Gudunmawar da ta dace wajan ciyar da Addinin Musulunci gaba, Karkashin Jagorancin Shugabansu Na kano Sheikh Malam Mua'z.

Sannan Maimartaba Sarki Ya shirya Musu liyafa, tare da Karramasu.