ACOSHTECK Ta roki Gwamnatin Jihar Katsina Ta Bude Sauran Makarantun Kiwon Lafiya Da Suka Cika Ka'ida.

top-news

Auwal Isah Musa (Katsina Times)

Kungiyar kula da tafiyar da harkokin makarantun kiwon lafiya masu zaman kansu na jihar Katsina, ACOSHTECHK, ta roki gwamnatin jihar Katsina da ta bude sauran makarantun kiwon lafiya da suka cika ka'ida bayan da aka dakatar da su.

Shugaban kungiyar, Tukur Shehu ne ya yi wannan rokon a yayin da kungiyar ta kira wani taron manema labarai a ranar Litinin din nan, KatsinaTimes ta ruwaito.

Tun farko, shugaban ya fara da godiya da yaba wa gwamnatin jihar kan matakan da ta dauka na rufe daukacin makarantun a karon farko, ta gudanar da bincike ta kuma tantance wadanda suka cika ka'ida, sannan ta bude wasu a matsayin rukunin farko.

"Muna yaba wa gwamnatin jihar katsina bisa ga kokarin da ta yi na tsarkake wannan harka ta koyar da kiwon lafiya a jihar katsina. Saboda makarantun nan da aka bi su aka tantance su, hanya ce da aka tsarkake harkar kiwon lafiya a jihar katsina."

"Su ma kwamitin da aka nada suka yi aikin tantancewar, mun san sun yi bakin kokarinsu, kuma sun nuna adalci." In ji shi.

Tukur shehu ya ce, duk da haka kungiyar tasu tana roko ga gwamnati da kuma kwamitin tantancewar, da su tantance sauran makarantun da ba a tantance ba a rukunin na farko da ba su cika wadansu ka'idoji ba, inda ya ce yanzu sun cika ka'idojin domin har sun mika takardar cika ka'idodin.

"Muna kira ga wannan kwamiti ya yi kokari ya bude sauran makarantun da bai bude ba tun da sun samar da abubuwan da suke bukata na koyarwa domin su ci gaba da gudanar aikace-aikacensu. Saboda rashin hakan, na iya shafar dalibansu."

Kungiyar ta ACOSHTECHK ta kara bayyana irin gudummuwar da makarantun nasu suka kawo wajen ci gaban harkar kiwon lafiya a jihar, inda suka bayyana cewar da yawansu sun samu tantancewa gami da lasisi gudanar da harkokin kiwon lafiya ga hukumomin lafiya daban-daban.

A la'akari da haka, kungiyar ta shawarci gwamnatin jihar katsina da cewar, ta duba lamarin gurabun wadanda suka aje aiki domin cike su da wadannan yara wadanda da yawansu ba su da aiki yi.

Tukur shehu, ya kuma yi kira tare da gargadar duk wani mai sha'awar shiga cikin harkar kiwon lafiya ko bude makarantar koyar da kiwon lafiya, da cewar ya tabbatar da ya bi ka'idoji, kuma ya je ma'akatar kiwon lafiya domin ya samu tantancewa tukunna.

Daga karshe, kungiyar ta ACOSHTECHK ta kara shawartar gwamnatin jihar cewar, ganin yadda jihar ke da 'pharmacy technicians' a cikinta,   to gwamnatin ta rika siyan sinadarai na hada magunguna a wajensu sai a rika hada su a asibitoci kamar yadda wasu gwamnatocin baya suka yi don ci gaban harkar kiwon lafiya a jihar, a maimakon siyowa daga waje.