GWAMNA DAUDA LAWAL YA ƘADDAMAR DA AIKIN HANYA A RIBAS, YA JINJINA WA GWAMNA FUBARA

top-news

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yaba wa ƙoƙarin Gwamna Siminalayi Fubara kan ayyukan raya ƙasa daban-daban a Jihar Ribas.

Gwamna Lawal ya kasance babban baƙo na musamman a wajen ƙaddamar da aikin titin da gadojin Opobo, wanda ya gudana a ranar Litinin a ƙaramar hukumar Opobo/Nkoro.

Da yake gabatar da jawabinsa a wajen ƙaddamar da aikin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa kammala aikin titin Opobo da gadoji ya nuna yadda Fubara ke da himma wajen bunƙasa ababen more rayuwa da inganta zamantakewa da tattalin arziki da jin daɗin al’ummar jihar Ribas.

“Ci gaban ababen more rayuwa, kamar yadda muka sani, wani ginshiƙi ne na ci gaban tattalin arziki da ci gaban al’umma. Hanyar Opobo da tare da gada babu shakka za ta ƙara samar da haɗin kai, inganta kasuwanci, da sauƙaƙe samun dama ga muhimman ayyuka ga mazauna Opobo da kewaye.

“Samar da ingantattun hanyoyin sufuri zai haifar da ayyukan tattalin arziki da kuma buɗe sabbin damarmaki ga al’ummomi a ciki da wajen jihar. Ingantattun ababen more rayuwa tabbas za su jawo hannun jari, da bunƙasa yawon buɗe ido, da ɗaga darajar al'ummar Opobo a idon duniya”

Gwamna Lawal ya ci gaba da nanata cewa Gwamna Fubara ya jajirce wajen ganin gwamnatinsa ta kawo sauyi ga ci gaban zamantakewa da tattalin arziki a jihar Zamfara.

“Muna da ra’ayi ɗaya cewa ingantattun ababen more rayuwa su ne ginshiƙi wajen raya ayyukan tattalin arziki da kuma ɗaukaka matsayin rayuwar jama’armu. A Zamfara, muna samun ci gaba mai ban mamaki ta hanyar ginawa da kuma gyara wasu muhimman ayyuka a faɗin jihar.

“Filin jirgin sama na Gusau da ke gudana, da kuma gina babbar hanyar sadarwa ta karkara da birane, shaida ne ƙarara kan burinmu na ingantawa da kuma zamanantar da muhimman ababen more rayuwa don inganta rayuwar al'ummarmu. Waɗannan ayyukan sun daidaita tare da hangen nesa namu don ƙirƙirar dama da kafa tushe mai ƙarfi don samun ci gaba mai ɗorewa.

“Ina yaba wa Gwamna Fubara bisa jajircewarsa na ci gaban jihar Ribas. Wannan sadaukarwar da ya yi don samar da makoma mai kyau ga jama'arsa abu ne mai ban sha'awa da gaske kuma abin koyi ne ga sauran jihohi.

“Har ila yau, ina gode masa saboda karramawar da aka yi min na kasancewa cikin wannan gagarumin taron. Ina da yaƙinin cewa hanyar Opobo da gadoji za su kawo wa al’ummar Opobo alfanu mai ɗorewa tare da ba da gudummawa sosai ga ci gaban jihar Ribas baki ɗaya.”

Tun da farko Gwamna Siminalayi Fubara ya nuna jin dafinsa ga Gwamna Lawal bisa amsa gayyatar da aka yi masa na zama babban baƙo.

Gwamna Fubara ya bayyana cewa gwamnatin da ta gabata ta ƙaddamar da aikin gina titin zobe na Opobo da gadoji a ranar 28 ga Mayu, 2023. “Mun ɗauki nauyin sake fasalin aikin tare da ɗaukaka shi zuwa matsayin da yake a yanzu. Wannan aikin yana da muhimmanci a gare ni, kuma na yi farin cikin ƙaddamar da shi.”