Gwamna Radda Ya Dauki Matakin Farfado da Ma'aikar Buga Takardun Gwamnatin jiha.
- Katsina City News
- 16 Dec, 2024
- 59
Maryam Jamilu Gambo, Katsina Times
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya dauki mataki mai karfi don farfado da Sashen Buga Takardun Gwamnatin Jihar Katsina. Wannan yunkuri na da nufin inganta yadda ake gudanar da ayyukan cikin gida, samar da karin hanyoyin samun kudin shiga, da karfafa kwazon cibiyoyin cikin gida.
A bisa umarnin Gwamnan, dukkan ma’aikatu, hukumomi, da cibiyoyin gwamnatin jiha an umurce su da yin amfani da ayyukan wannan sashen buga takardun na gwamnati. Wannan mataki yana da nufin magance matsalar buga muhimman takardu masu alaka da tsaro a gidajen buga takardu masu zaman kansu.
Daraktan Janar na Sashen Buga Takardun Gwamnati, Abba Rufai Musawa, ya yaba da wannan mataki na Gwamnan. Tun bayan da ya karbi ragamar jagoranci, Musawa ya gudanar da ziyarce-ziyarce na musamman zuwa jihohi makwabta, inda ya shiga tsare-tsaren nazari na aiki don kwatanta da kuma inganta ayyukan sashen.