GWAMNAN LAWAL YA JADDADA ƘUDURINSA NA BAIWA ƁANGAREN SHARI'A 'YANCIN KANSU DON SAMAR DA ADALCI A ZAMFARA
- Katsina City News
- 03 Dec, 2024
- 27
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta duƙufa wajen ba da fifiko ga tsare-tsare da ke inganta tabbatar da adalci a kan lokaci da kuma kare ’yancin ɓangaren shari’a.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Litinin ɗin da ta gabata a wajen taron ƙara wa juna sani ga alƙalai da ma’aikatan kotuna a babbar kotun shari’a ta Jihar Zamfara, wanda aka gudanar a harabar babbar kotun da ke Gusau.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, taron ya samar da wata dama ga jami’an shari’a da masu ruwa da tsaki domin tantance ayyukan da bangaren shari’a ke yi, da gano ƙalubale, da kuma kafa sabbin manufofi.
A jawabinsa na bufe taron, Gwamna Lawal ya amince da jajircewa da jagoranci na ƙwarai na Babbar Alƙalin Alƙalan Jihar, Mai Shari’a Kulu Aliyu, OFR, FNJI, da ɗaukacin bangaren shari’a bisa jajircewarsu na sauke nauyin da aka ɗora musu.
Ya ce, “jajircewarta wajen tabbatar da adalci yana ƙara ƙwarin gwiwa da kuma ƙara wa bangaren shari’a aminci a matsayin wata cibiya mai muhimmanci a tsarin dimokuraɗiyya. Wannan gwamnati ta tsayu tsayin daka wajen tallafa wa bangaren shari’a a dukkan ayyukanta.
"Gwamnatina za ta ci gaba da ba da fifiko ga shirye-shiryen da za su inganta samar da adalci a kan lokaci da kuma kare 'yancin wannan bangare na gwamnati."
Gwamna Lawal ya bayyana cewa, taron ƙara wa juna sanin na da matuƙar muhimmanci. “Zai inganta fasaha da kuma ilimantar da mahalarta domin su kasance cikin shiri sosai don yin hidima da biyan buƙatun jama’a. Jama'ar mu na kallon ku a matsayin matita ga talakan ƙasa wajen ganin ya samu adalci tare da kare haƙƙinsa. Dole ne jami'an shari'a da ma'aikatan su kasance cikin shiri sosai don cimma waɗannan manufofi, musamman a waɗannan lokutan da ake fuskantar ƙalubale.
“Babbar Alƙalin Alƙalai, alƙalan babbar kotun jihar Zamfara, manyan mahalarta taron, abin farin ciki ne ganin irin matakan da hukumar shari’a ke ɗauka wajen tsare-tsaren ma’aikatan Majistare da sauran ma’aikatan shari'q domin tabbatar da adalci.
Gwamnan ya kuma buƙaci bangaren shari’a da su yi taka-tsan-tsan a kan wasu ’yan tsirarun da ɗabi’unsu za su iya gurgunta mutuncin wannan hukuma. "Ganowa tare da magance rashin ɗa'a a bangaren wani nauyi ne da ke buƙatar himma, mutunci, da sadaukarwa."