Gwamnatin Tarayya Ta Fara Karbar Harajin N50 Daga Harkokin Kasuwancin Intanet

top-news

Gwamnatin Tarayya ta sanar da fara karbar harajin N50 daga dukkan cinikayyar intanet da ta kai N10,000 ko fiye, wanda aka yi ta amfani da dandamalin fasahar hada-hadar kudi (Fintech) irin su Opay, Moniepoint, Kuda da sauransu.

Harajin, wanda aka sani da Harajin Canja Wurin Kudi ta Intanet (EMTL), an bullo da shi a karkashin Dokar Kudi ta 2020, inda ake karbar kudin N50 a kan duk wanda aka aika wa kudi ta hanyar intanet da ya kai N10,000 ko sama da haka, a matsayin kudin sau daya kawai.

A cikin wata sanarwa da Opay ta fitar ga kwastomominta a watan Satumba, ta bayyana cewa wannan harajin Hukumar Tara Kudaden Haraji ta Gwamnatin Tarayya (FIRS) ce ta gindaya, tare da jaddada cewa kamfanin ba shi da wani riba daga kudin.

"Ku sani cewa daga ranar 9 ga Satumba, 2024, za a fara karbar harajin N50 a kan dukkan cinikayyar intanet da ta kai N10,000 ko sama da haka, wadda aka biya a cikin asusun mutum ko na kasuwanci, a cewar dokokin Hukumar Tara Haraji (FIRS)," in ji sanarwar Opay.

Opay ta kara da cewa, "Muhimmiyar sanarwa ita ce cewa mu ba mu amfana da wannan kudin a kowace hanya, saboda an ware shi kai tsaye don gwamnatin tarayya."