Mataimakin Shugaban Ƙasa Ya Isa Katsina Ziyarar Ta’aziyya
- Katsina City News
- 23 Nov, 2024
- 145
Mataimakin Shugaban Ƙasa na Tarayyar Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ya isa Jihar Katsina a yau domin isar da ta’aziyyarsa ga gwamnatin jihar da al’ummar Katsina kan rasuwar wasu manyan jiga-jigai biyu Talbana Katsina Ambassador Zakari Ibrahim, Da Marigayi Maradin Katsina Hakimin Gundumar Kurfi a jihar.
Mataimakin Shugaban Ƙasa ya sauka a Filin Jirgin Sama na Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina, inda Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya tarbe shi cikin girmamawa. Hakazalika, wasu manyan jami’an gwamnatin Radda sun halarci tarbar.
Yayin ziyarar ta’aziyyar, Sanata Shettima ya bayyana muhimmancin haɗin kai da juriya yayin da ake fama da rashin manyan mutane masu tasiri. Ya yaba wa irin gudunmawar marigayin da suka bayar wajen ci gaban Jihar Katsina da Najeriya baki ɗaya, yana mai bayyana rasuwar su a matsayin babban rashi ga ƙasa.
Ana sa ran Mataimakin Shugaban Ƙasar zai gana da iyalan marigayin don isar da ta’aziyyarsa kai tsaye.