DANKANTAKA TSAKANIN KASAR KATSINA DA ZAZZAU.
- Katsina City News
- 22 Nov, 2024
- 240
Kasar Katsina da Kasar ZAZZAU, suna daga cikin kasashen Hausa, da a Tarihance ake ce masu Hausa Bakwai. Kamin Jihadin Shehu Usman Danfodio na karni na (19) kasashen Hausa suna cikin rudin yake yake a tsakanin su, wannan Gari Yana yakar wannan, wanna Yana yakar dan uwanshi. Anshi yin Yaki tsakanin Katsina da Gobir, ko Katsina da Kano da sauransu. Amma ba a samu wani cikakken bayani ba game da Yaki tsakanin Kasar Katsina da ZAZZAU.
Dangantakar data fi karfi tsakanin Kasar Katsina da Zazzau itace ta harkar Kasuwanci da ilimi.
1. Idan muka dawo kan ilimi, acikin farkon Karni na 16 zuwa na 17, Kasar Katsina ta kasance babbar centre ta koyar da ilimin addinin Musulunchi a Kasar Hausa, a sabili da manyan Malaman addinin Musulunchi da Kasar Katsina ta Tara a wancan Lokacin irin sun Danmarna, Dantakun, Dan Masani da sauransu. Wannan yasa baki daga bangare daban daban na Kasar Hausa suna zuwa neman ilimi a Kasar Katsina, a wannan lokacinne Mutanen Zazzau suka rika huddatayya ta neman tsakanin su day mutanen Katsina.
Ta bangaren ilimin Boko, a cikin shekarar 1922 ne aka bude Katsina College wadda ta zama teacher training College ta farko a Tarayyar Nigeria. An samu Dalibai da dama daga fadin Arewacin Nigeria da suka halarci Katsina College daga cikinsu akwai Alhaji Nuhu Bamalli( Regional Minister ) da sauransu. Daga baya kuma aka dauke Katsina College aka maidata Kaduna, Wanda kuma daga baya ta koma Zaria, da sunan " BAREWA COLLEGE ZARIA". A Wannan lokacin Dalibai da dama daga Katsina sun halarci BAREWA College daga cikinsu akwai, General Hassan Katsina, akwai Sardaunan Katsina Alhaji Ibrahim Kumasi da sauransu, wannan yaka alaka ta kirki tsakanin Mutanen Katsina da Zazzau. Haka kuma a lokacin mulkin Premier Arewa Sir Ahmadu ( Sardauna) aka bude Jamiar Ahmadu Bello a Zaria, dalibai da dama daga Katsina sun halarci Jamiar a Zaria daga cikin su akwai Shugaban Kasar Nigeria Ummaru Musa Yar"arua da sauransu.
Idan muka duba gidajen Sarautar A yanzu guda hudu ne (4). Akwai 1. Mallawa, 2. Barebari, 3. Sullubawa da 4, Katsinawa. Gidan Sarautar Zazzau na Katsinawa asalinsu Katsinawa ne kamar yadda sunan su ya nuna, misali Marigayi Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya fito daga Gidan Sarautar Zazzau na Katsinawa, wannan ya Kara babbar dangantaka tsakanin Katsina da Zazzau.
2. Ta bangaren Kasuwanci akwai huddatayya Mai kyau tsakanin mutanen Zazzau da Katsina tun lokacin Sarakunan Habe ana Kasuwancin Sahara( Transharan Trade). Kasar Katsina ta kasance babbar centre ta Kasuwanci a Kasar Hausa tsakanin Karni na 16 zuwa na 18, wannan yasa manyan Kasashe suka rika hudda da Katsina ta harkar Kasuwanci. A wannan lokacin Kasar Katsina tayi hudda ta Kasuwanci da Kasar ZAZZAU.
Haka kuma acikin Karni na (19) Mujaddadi Shehu Usman Danfodio ya raba Tutoci ga shuwagabanin Jihadi a Kasar Hausa. A Katsina Sarkin Katsina Malam Ummarun Dallaje shine ya Zama babban Jagora na Jihadin, hakanan kuma Sarkin Zazzau Suleiman shine babban Jagora na Jihadi a Kasar Zazzau. Kamar yadda aka Kori Sarakunan Habe a Katsina suka gudu suka koma Maradi, inda suka kafa Sarautar Sarkin Katsina Maradi, to haka suma Zazzau da aka Kore Haben sai suka gudu suka koma Abuja, suka kafa Masarautar su acan. Bayan cin nasarar Yaki anci gaba huddatayya tsakanin Kasar Katsina da Zazzau, akwai alaka ta huddar Kasuwanci a wancan Lokacin tsakanin Amir Katsina da Amir .Zazzau.
Alh. Musa Gambo Kofar soro.