Ministan tsaron Nijeriya ya yaba da horon da cibiyar yaki da ta'addanci ta IMCTC ta ba sojojin Nijeriya
- Katsina City News
- 19 Nov, 2024
- 188
Ministan kasa a ma'aikatar tsaron Nijeriya, Dr Bello Mohammed Matawalle, ya bayyana godiyarsa ga babban sakataren cibiyar hadin kan yaki da ta’addanci ta Musulunci IMCTC kan horon da ake ba sojojin Nijeriya domin karfafa guiwarsu wajen yakar ta’addanci.
Dr Matawalle ya bayyana hakan ne a ziyarar aiki da ya kai hedikwatar IMCTC da ke birnin Riyadh na kasar Saudiyya.
Ziyarar ta kara jaddada kudirin Nijeriya na ci gaba da bunkasa karfinta na tsaro da kuma karfafa hadin guiwar kasa da kasa wajen yaki da ta'addanci.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai taimaka wa Ministan kan harkokin yada labarai, Ahmad Dan-Wudil, a Abuja ranar Talata, Dr. Matawalle ya bayyana gagarumin tasirin horarwar da cibiyar ta IMCTC ga sojojin Nijeriya.
“Irin horaswa daban-daban da cibiyar ta IMCTC ta bayar sun taimaka matuka wajen inganta kwazon dakarun mu na yaki da ta’addanci,” inji Dr. Matawalle.
Ya yaba da kudurin cibiyar na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya tare da jaddada ci gaba da hadin guiwar Nijeriya da cibiyar.
A yayin ziyarar tasa a Saudiyya, Dr. Matawalle zai kuma gana da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman.
Ana sa ran ganawar za ta mayar da hankali ne kan karfafa alakar da ke tsakanin Nijeriya da Saudiyya, musamman a fannin hadin guiwa a fannin tsaro da yaki da ta'addanci.
IMCTC mai hedikwata a Riyadh, kawancen gwamnatoci ne na kasashen musulmi da suka sadaukar da kansu wajen yaki da ta’addanci ta hanyar musayar bayanan sirri, horarwa, da ayyukan hadin gwiwa.
Nijeriya ta kasance mai taka rawar gani a cikin kawancen, inda take cin gajiyar shirye-shiryenta na dabaru da nufin tunkarar barazanar ta'addanci.
Horon da cibiyar ta IMCTC ta bayar ya taimaka wa Nijeriya daukar dabarun yaki da ta’addanci na zamani da kuma inganta hadin guiwar hukumomin tsaro a tsakanin sojojin kasar.
A halin da ake ciki, tun lokacin da ministan tsaro ya hau karagar mulki, rundunar sojin Nijeriya ta samu gagarumin ci gaba wajen dakile ayyukan ta'addanci, sakamakon hadin guiwa da kungiyoyin kasa da kasa kamar IMCTC.
Ana kallon ziyarar ta Ministan a matsayin wani mataki na karfafa wadannan kawance da kuma lalubo sabbin hanyoyin hadin gwiwa.
"Wadannan haɗin guiwar na da matukar muhimmanci ga zaman lafiyar yankin da kuma yaƙi da ta'addanci a duniya," in ji wani mai sharhi kan harkokin tsaro a Abuja.
Ana sa ran ziyarar aikin Dr Matawalle a Riyadh zai karfafa kawancen tsaron Nijeriya na kasa da kasa, da tabbatar da cewa kasar ta ci gaba da kasancewa a sahun gaba wajen yaki da ta’addanci da kuma samar da zaman lafiya a duniya.