NNPCL ta dakatar da shigo da fetur na Naira tiriliyan 24, tana kuma samun kayan daga matatar Dangote kai tsaye.
- Katsina City News
- 12 Nov, 2024
- 143
Mele Kyari Ya ce, “A yau, NNPC ba ta shigo da kowanne kaya ba, daga matatun gida kawai muke karba.”
Kyari ya karyata jita-jitar da ke cewa NNPC na kawo tangarda ga ayyukan matatar Dangote.
“Ba haka abin yake ba, kuma zan bayyana hakan a fili. Muna alfahari da kasancewa masu hannun jari a matatar Dangote, babu shakka. Mun ga dama cewa akwai kasuwa mai kyau da zata iya karɓar ganga 300,000 na manmu; mun san cewa nan gaba mutane za su fara samun kalubale wajen samun kasuwannin siyar da mai.
“A yau, NNPC ba ta shigo da kowanne kaya ba, daga matatun cikin gida kawai muke karba. Amma kuma na san cewa muna aiki tare da gwamnati don tabbatar da cewa mun magance batun farashi idan muka dogara da kasuwar cikin gida wajen samun dukkanin kayayyakinmu. Wannan zai iya zama kalubale amma muna kan hanya wajen magance shi. Zan iya tabbatar da cewa an samu ci gaba mai kyau kuma wannan ba zai zama matsala ba.”