UNGUWAR CIKIN GIDA.
- Katsina City News
- 10 Nov, 2024
- 111
Wannan Unguwa tana a tsakiyar Birnin Katsina. Ana kiranta da wannan suna domin tana cikin dairar Gidan Sarkin Katsina watau Gidan Korau. Wasu bayanai sun sun nuna cewa an kafa wannan Unguwar bayan an Gina Gidan Sarkin Katsina cikin Hijira ta 1348 miladiyya.
. Akwai shiyyoyi da dama cikin Unguwar cikin Gida irinsu, Unguwar Gadi, da Garjagau da Unguwar Kuka da Unguwar Tsamiya da Lungun Tafkin Lambu. Gameda Unguwar Gadi, sunan ta ya samo asline daga wani babban Dogarin Sarki Dikko mai suna Alin Gadi. Shi Alin Gadi Mutumin Kasar Mani ne. Alin Gadi Yaron Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ne tun ma kamin Dikkon ya zama Sarkin Katsina. Lokacin da Sarki Dikko ya zama Sarki a 1906 Sai ya dauko Alin Gadin data Kasar Mani, ya maido shi cikin Gida, ya Kuma bashi gida a wurin da yanzu ya zama Unguwar Gadi. Saboda muhimmancin Alin Gadi, Sai Unguwar ta amsa sunansa na Unguwar Alin Gadi, Wanda daga baya aka takaita shi zuwa Unguwar Gadi. Amma tun kamin zuwan Alin Gadi akwai mazauna a wurin, Sai zuwan shi aka rika Kiran wurin da sunan Alin Gadi.
Akwai zuruar Tarno Barka a Unguwar Gadi, Wanda shi Tarno Barkan mutumin Maiduguri ne, yazo tun lokacin mulkin Dallazawa, daga cikin Zuruar Tarno Barka akwai Malam Goje, da Isiyaku Turaki Mahaifin Turaki Sani Store, da Guda, da sauransu. Da dai sauransu.
Sai Unguwar Garjagau ta cikin Gida. Unguwar Garjagau tana nan a cikin Gida Arewa da Gidan Korau na Sarkin Katsina. Asalin wadanda suka Fara zama a wannan Unguwa sune zuruar Badawa daga Kasar Bade. Wanda suka taso daga Rimin Badawa suka dawo Garjagau cikin shekarar 1861. Bayani ya nuna cewa kalmar Garjagau Kalma ce wadda a harshen Badanci take nufin matsuguni, wato wurin zama. Daga cikin Zuruar Badawan da suka tashi a Garjagau akwai Alhaji Mamman Dawai, da Alhaji Abu Bazariye da Dr. Ahmed Magaji da sauransu.
Ita Kuma Unguwar Tsamiya tana nan Bayan Gidan Korau. A wannan Unguwa ta Tsamiya akwai manyan Gidaje kamar Gidan Matazu Agawa, Gidan Yari Ammani da Gidan Sarkin BINDIGA da sauransu. A Unguwar Tsamiya dinne Kabarin Ummarun Dallaje yake. A dai dai Kabarin Ummarun Dallaje akwai sauran wasu Kaburbura na Sarakunan Dallazawa, wadanda suke nan bayan Gidan Sarki a Tsamiya. Akwai Kuma Kabarin Galadima Dudi, Wanda Yana daya daga cikin manyan aminnan Ummarun Dallaje.
Akwai Kuma Unguwar Kuka. Yawancin Mazauna Unguwar Kuka ta cikin Gida aminai ne na Sarki, musamman Sarki Dikko, Wanda saboda aminci dake tsakaninsu ya Basu Sarautar Ajiya wadda aka ba Miya, wato Ajiya Miya. Daga Ajiya Miya Sai Ajiya Danladi, Sai Ajiya Atija, Sai Ajiya Abubakar da sauransu, duk dai anan Unguwar Kukar. Kuma a Zamanin Sarki Dikko har zuwa Sarki Kabir Usman.
Akwai Kuma Lungun Tabkin Lambu. Shi Kuma asalin shi Lambu ne na Sarkin Katsina Muhammadu Dikko (1906-1944). Daga cikin Lambune Sarki Dikko ya shifka wani Dabino yace idan ya rasu a kawo shi a rufeshi kusa da Dabinon, haka Kuma akayi a shekarar 1944. Daga cikin Sarakunan da aka rufe a Tabkin Lambu na Sarki Dikko akwai Sarkin Katsina Muhammadu Dikko, Sarkin Katsina Sir Usman Nagoggo, Sai Sarkin Katsina Muhammadu Kabir da Kuma Matansu. Ita Makabartar Tabkin Lambu ana rufe Sarakunan Sullubawa ne kawai da Matansu, Amma baa rufe yayan Sarki a ciki.
Alhaji Musa Gambo Kofar soro.