Gwamna Radda Ya Kaddamar da Tashoshin KTSTA a Mashi da Ingawa
- Katsina City News
- 07 Nov, 2024
- 249
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya kaddamar da sabbin tashoshi na hukumar sufuri ta jihar, KTSTA, a kananan hukumomin Mashi da Ingawa.
A wajen kaddamar da sabbin tashoshin da aka yi a hedikwatar kananan hukumomin biyu, Gwamna Radda ya ce tashoshin za su zama wuraren ajiye motoci da diban fasinjoji daga kananan hukumomin biyu har ma da makwabtansu.
Ya ce fadada ayyukan KTSTA zuwa wasu sassan jihar na da nufin saukaka sufuri ga 'yan jihar a cikin wannan yanayin na hauhawar farashin man fetur.
Gwamnan yace duba da hakan yasa hukumar ke yin rangwame ga matafiya da nufin samar musu saukin farashin sufuri.
Ya kuma yaba ma hukumar KTSTA karkashin jagorancin Alhaji Haruna Musa Rugoji bisa hobbasan da yake yi wajen inganta harkokin hukumar ta fuskoki daban daban.
A nasa jawabin, shugaban hukumar ta KTSTA, Alhaji Haruna Musa Rugoji, ya ce an tsara sabbin tashoshin ne da manyan wuraren ajiye motoci da ofisoshi da manyan harabobi da dakunan jira na matafiya.
Ya bayyana cewa sabbin tashoshi biyu za su rage cunkoso a tashoshin hukumar da ke Daura da Katsina, baya ga samar da waje da motocin hukumar zasu rika yada zango.
Alhaji Musa Rugoji ya ce har ila yau hukumar na shirin kaddamar da wasu sabbin tashoshi a wasu manyan garuruwan jihar domin kusanto da harkar sufuri ga matafiya a duk sassan jihar.
Ya ce hukumar za ta ci gaba da sayen sabbin motoci lokaci zuwa lokaci domin samar da karin kudaden shiga ga gwamnatin da kuma samar da sufuri a farashi mai rangwame ga al’ummar jihar.