Hukumar CSDA Ta Gudanar Da Taron Bita Na Bayar Da Horon Aiki Ga Wasu Yankuna A Katsina

top-news

Daga Sulaiman Ciroma

Hukumar CSDA ta gudanar da taron bayar da horo na bada tallafin ayyukan jinkai ga kananan hukumomi a jihar Katsina.

Taron ya kasance matakin karshe da hukumar ke aiwatarwa wajen bayar da tallafi ga al’ummah domin bada kyakkyawan horo don samun ingantaccen aiki, kama daga hanyoyin da ya kamata abi wajen kasha kudade domin sayo kayan aiki da sauransu.

Yayin gudanar da horon, hukumar ta gabatar da bayar da cek na kudade ga shugabannin ko wace karamar hukuma don fara gudanar da ayyuka a kowane yanki.

Shugaban Hukumar, Muhammad Dikko Abdul’aziz yayi tsokaci inda yak e jaddada kyakkyawan aniyar hukumar na tsayawa tsayin daka wajen ganin ta tallafawa al’ummah domin wannan yanayi da ake ciki, shugaban ya yi jan kunne ya kuma shawarci shugabannin gudanar da ayyukan wajen ganin an gudanar da wadannan ayyuka yadda ya kamata.

Haka kuma shugaban ya kara da cewa “Wannan aiki abu ne da aka daura muku mai wuya, duk abinda aka ce an dora maka amana kuma aiki ya hadu harda kudi ciki to sai ka jajirce. Kamar yadda mai girma Gwamna ya yarda da wannan hukuma ta mu ya yarda cewa yana bada kudi ta hannunmu muna ba ‘yan kwamuniti muna lura da irin ayyukan da suke yi kuma muka tsaya tsayin daka kan wannan aiki na amana da sadarwa to ya kamata idan tazo hannunku kuyi shi bisa ga amana ku dauka wannan aiki ne na hidima wa al’ummah.

Mukaddashin manajan ayyuka, Injiniya Abbas Sulaiman Audi yayi Karin haske inda ya gabatar da kasida kan yadda ya kamata a dunga kula da ayyukan yayin gudanarwa domin samun ingantaccen aiki.

Daga cikin shuwagabannin hukumar da suka halarci bayar da horon akwai manajan kudi da harkokin mulki Alhaji Magaji Yusuf Bakori, sannan akwai mukaddashin manaja na M.E Ibrahim Dandela, akwai kuma Jami’I mai kula da harkokin ilmantarwa da horaswa Samaila Balarabe, tare da su kuma akwai Malama Rumasa’u wacce take mataimakiyar accountant da Malama Habiba Abubakar jami’a mai kula da harkokin mata, sannan sai Odita na hukumar Malam Ahmed Rabi’u Kankia, sai kuma jami’in harkokin Saye-Saye Alhaji Aminu Hassan Gafai.

Idan ba a manta ba dai a kwanakin baya wannan hukuma ta gudanar da zaben tantance bukatu wanda ake kira a turance da “Patispatory Rural Appraisal” ya kasance zabe ne da wannan hukuma ke gudanarwa a kowani yanki da ya kamata a tallafawa domin gano aikin da za a gudanar daidai da bukatun al’ummar yankin.