Mu'assasatul Khairiyya da hukumar Hisbah A Katsina Sun Tallafawa Mata da Suka Tuba daga Aikata Baɗala
- Katsina City News
- 03 Nov, 2024
- 130
Muhammad Aliy Hafiziy (Katsina Times)
A ranar Asabar, 2 ga Nuwamba, 2024, Mu'assasatul Khairiyya tare da hadin gwiwar Hukumar Hizbah ta Jihar Katsina sun gudanar da taron yaye mata goma da suka shiriya daga aikata baɗala, sun kuma tallafa musu domin su samu kafar rayuwa mai tsafta. Taron ya gudana ne a dakin taro na Katsina Motel, tare da halartar manyan jami'ai da 'yan siyasa na jihar, ciki har da Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Farouk Lawal Jobe; Hajiya Asma'u Farouk Lawal Jobe; Malam Hadi Balarabe; Alhaji Aminu Abdullahi Yammawa; Malam Ibrahim Mai Gora; Justice Musa Danladi; da tsohon Mataimakin Gwamna, Alhaji Tukur Jikanmshi, shugabar cibiyar Ma'assasatu Khairiyah Hajiya Hauwa Radda, da sauran shugabanni masu daraja.
Da yake gabatar da jawabi a wurin taron, Shugaban Hukumar Hizbah ta Jihar Katsina, Dr. Aminu Usman Abu Ammar, ya bayyana cewa matan da aka tallafawa sun kasance daga cikin wadanda hukumar ke kira da yi masu nasiha kan dabi’un rayuwa mai kyau. Ya ce, "A tsawon lokaci, hukumar Hizbah ta ci gaba da yi musu wa’azi da shawara, amma sai aka ga dacewar tallafawa su yadda za su samu damar koyarwa da ciyarwa don su samu cikakkiyar nasara. A wannan lokacin, Hajiya Hauwa Umar Radda ta dauki nauyin daukar nauyin rayuwarsu, tana ciyar da su safe, rana da dare, don ganin sun samu dama ta cikakkiyar natsuwa da koyarwa.”
A nasa jawabin, Mataimakin Gwamna, Alhaji Farouk Lawal Jobe, ya yaba da wannan aiki na taimako da kungiyoyin suka yi, tare da nuna goyon bayansa ga kokarin da Hukumar Hizbah ke yi wajen hana aikata munanan dabi’u a cikin al’umma. Ya kuma yi kira ga iyaye su maida hankali wajen tarbiyyar 'ya'yansu don rage yawaitar abubuwan da ke kawo lalacewar al'umma.
Bayan haka, an bayar da tallafi na musamman ga matan, ciki har da kekunan dinki ga mata guda uku da injinan markade ga mata guda bakwai, tare da kayan karatu kamar Qur’ani da abubuwan ibada. Haka nan, an kuma raba kayan masarufi da suka hada da abayu, turamen atamfa, da buhunan filawa domin taimakawa wajen farfado da rayuwarsu. Bugu da kari, Mu'assasatul Khairiyya ta ba kowane daga cikin matan tallafin Naira dubu dari, yayin da shi ma Mataimakin Gwamna, Alhaji Farouk Lawal Jobe, ya ba su kyautar Naira dubu dari-dari a matsayin kari.
A jawabin karshe, malamai da shugabannin addini sun yi wa matan nasiha, inda suka bukace su da su kiyaye mutuncinsu da na addininsu, tare da tabbatar da tabbatacciyar tuba da bin sahihin hanya. An yi addu'ar cewa su zama masu tsayin daka wajen gudanar da rayuwarsu ta cikin tsafta da kaunar zaman lafiya a cikin al'umma.