Yara Matasa da Suka Yi Zanga-zangar Yunwa Sun Yanke Jiki sun fadi a Kotu Kafin Shigarsu Gaban Alƙali
- Katsina City News
- 01 Nov, 2024
- 210
An samu wasu yara matasa guda biyar da suka yanke jiki suka fadi yayin da ake shirin fara shari'arsu a Babbar Kotun Tarayya dake Abuja a ranar Jumma’a.
Rahotanni sun bayyana cewa matasan, wadanda suke cikin mutane 125 da ake tuhuma, ana zarginsu da hannu a zanga-zangar #EndBadGovernance da aka gudanar a Jihar Kano. Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ce ta gabatar da su gaban kotu bisa wannan zargi.
An rarraba masu gabatar da kara zuwa rukuni biyu, na farko mai mutane 76, sai na biyu mai 49, domin fara shari’ar gaban Mai Shari’a Obiora Egwuatu.
A yayin da aka fara kiran rukuni na farko, wasu daga cikin matasan suka yanke jiki kafin su isa akwatin tuhuma.
A bisa wannan al’amari, alkalin ya dakatar da zaman shari'ar tare da kiran jami’an lafiya daga asibitin kotu domin su ba wa wadanda suka fadi kulawa ta gaggawa.
Lauyan masu kare kansu, Marshall Abubakar, ya bayyana cewa rashin abinci da rashin lafiya ne ya janyo faduwar yaran.
Ya ce: “Wadannan yara matasa suna fama da rashin lafiya da yunwa. Sun jima a tsare ba tare da kulawa ko abinci da magani ba. Suna bukatar kulawa ta musamman. Wannan ne ya haifar da wannan lamari mai ban takaici."