Malaman Firamare a Batsari Sun Koka Kan Rage Albashin Su Ba Tare da Cikakken Bayani Ba
- Katsina City News
- 31 Oct, 2024
- 239
Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
Malaman makarantar firamare a ƙaramar hukumar Batsari, jihar Katsina, sun yi ƙorafi mai tsanani kan rage albashin su na watan Oktoba, inda suka ce an yi haka ba tare da cikakken bayani daga hukumomin da suka dace ba. Rahotanni da *Katsina Times* ta samu sun tabbatar da cewa an cire wa sama da malamai 57 wani kaso daga albashin su, wanda ya haifar da fushi da kuma neman daukar mataki daga gwamnatin jiha.
Wani malami da ya nemi a ɓoye sunansa ya bayyana cewa, "Fiye da malamai 57 aka cire wa albashin watan Oktoba, amma ba mu samu wani gamsasshen bayani ba." Wata malama kuma ta bayyana cewa an cire mata N22,500 daga albashin ta na wannan watan ba tare da wani hujja ko laifi ba, tana mai kira ga gwamnatin jihar Katsina da hukumomin ilimi su gudanar da bincike domin tabbatar da adalci.
Rahotannin *Katsina Times* sun nuna cewa malaman da abin ya shafa suna fama da asara daban-daban, inda wasu ke rasa naira dubu goma, wasu dubu sha biyar, wasu kuma har naira dubu ashirin da biyu. Malaman sun bayyana wannan matakin a matsayin rashin adalci, tare da zargin yiwuwar an karkatar da kudin albashin su zuwa wata manufa.
Sakataren ilimi na ƙaramar hukumar Batsari, Malam Salisu Garba, ya tabbatar da cewa sun gudanar da rangadi a wasu makarantu kuma sun gano cewa malamai da dama basa zuwa don gudanar da aikin koyarwa. "Mun dauki wannan matakin ne domin inganta halin aiki, kuma duk malamin da ya kasa zuwa makaranta zai ci gaba da fuskantar hukunci," inji shi.
Sai dai wasu malamai sun musanta wannan ikirari, suna cewa suna halartar aiki a kai a kai kuma sun yi ikirarin cewa wannan matakin ba gaskiya ba ne. Sun kuma nemi gwamnatin jihar da hukumar ilimi ta jiha su binciki lamarin tare da duba wannan cire-cire da suka bayyana a matsayin ba bisa ka’ida ba.
Karamar hukumar Batsari na daga cikin wuraren da ke fama da matsalar tsaro a jihar Katsina, lamarin da ya sa aka rufe wasu makarantu a baya saboda hare-hare da satar mutane. Malaman makaranta sun nemi a gudanar da bincike domin tabbatar da adalci da kuma dawo da gaskiya kan albashin su da aka rage ba tare da cikakken bayani ba.