KAYAN GARGAJIYA NA MASARAUTAR KATSINA (KATSINA ROYAL REGALIA).
- Katsina City News
- 28 Oct, 2024
- 379
Kayan Gargajiya/Tarihi na Masarautar Katsina guda hudu ne.
1. Na farko shine TAKOBI GAJERE.
Ita wannan Takobi asalinta itace Takobin da Sarkin Katsina Korau ya yanka Sarki Sanau da ita, a lokacin ana Kokowa wajen Gasar Sarkin Katsina. Anyi wannan Kokowar acikin shekarar 1348, tsakanin Korau da Sanau. A inda shi Korau ya samu nasara akan Sanau ya yanka shi a gaban Jamaaa, Korau ya zama Sarkin Katsina Musulmi na farko. Ita wannan Takobi GAJERE Tarihi ya nuna Sarkin Katsina Muhammadu Korau yazo da ita Katsina. A bangare guda na Takobin an rubuta da Larabaci cewa ( There is no hero except Ali and no Sword except Dhulfakar) Maana babu wani Gwarzo Sai Aliyu sannan Kuma babu wata Takobi Sai Dhulfakar). Sannan Kuma a bangare guda na Takobin an rubuta da Larabac cewa ( Help from Allah and a speedy victory) maana Taimako daga Allah yake da Kuma nasara cikin Sauri. Wannan Takobin GAJERE itace Sarkin Katsina yake rikewa ga hannun shi a ranar Taron Sallah ko Durba. Kuma tana daya daga cikin Kayan Tarihin Katsina ( Katsina Royal Regalia).
2. Sai na biyu itace TUKUNYAR KARFE( Brazen Pot). Ita wannan TUKUNYAR ta Korau ce. Tarihi ya nuna Sarakunan Habe suna amfani da ita suna dafama mayakansu dauri a lokacin ana yake yake. Itama TUKUNYAR KARFE tana daya daga cikin Royal REGALIA na Katsina.
3. Sai na ukku itace Takobi Bebe. Ita wannan Takobin an kwace tane a fagen Yaki. Lokacin da akayi Yaki Tsakanin Katsina da Gobir a Shekarar 1795. Tarihi ya nuna Takobin Sarkin Gobir Yakuba ce, bayan KATSINAWA sun Kashe shi, Sai aka taho da Takobin Katsina. Ita wannan Takobin Bebe itace Sarkin Katsina yake ratayawa a Kafadar shi a ranar Taron Sallah ko Durba.
4. Sai na hudu shine Gwauren Tambari( THE BACHELOR DRUM). An kirashi Gwauren Tambari saboda yayi kowane Tambari girma a Tamburan Katsina sannan Kuma shi kadai ne bashi da danuwa, sannan Kuma baa kada shi Sai bikin nadin sabon Sarki ko Kuma daya daga cikin Hakimman Karagar ko Kuma Sarkin Sullubawa ko Gazobi a lokacin Habe da sauransu.
Shi wannan Tambari yayi kowane Tambari dadewa a Masarautar Katsina. Tarihi ya nuna a lokacin Sarakunan Habe idan zaa fita Yaki to Sai a hawo Itaciyar Bawada a rinka kada Gwauren Tambari.
A ranar Bikin nada Sabon Sarkin Katsina Galadiman Katsina zai kada Gwauren Tambari Sau 12. Haka Nan Kuma idan zaa nada daya daga cikin Hakimman Karaga kamar Galadima, Yandaka, Kaura, Durbi, ko Sarkin Sullubawa, to Sarkin Tambura zai kada Gwauren Tambari sau 3.
Wadannan sune cikakkun Kayan Gargajiya na Masarautar Katsina ( Katsina Royal Regalia).
Alh. Musa Gambo Kofar soro.