Gwamnatin jihar Katsina Da Zamfara sun yi ganawar Sirri da Ma'aikatar Tsaron Nijeriya
- Katsina City News
- 23 Oct, 2024
- 187
Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal da takwaransa na jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa sun yi wata ganawar sirri da Ministan tsaro Badaru Abubakar da mai bai wa shugaba ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribaɗu
Waɗannan ganawa guda biyu sun gudana ne a jiya Talata a ma'aikatar tsaro ta tarayya da kuma ofishin mai bai wa shugaban ƙasan shawara kan harkokin tsaro.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar yau, ya bayyana cewa taron ya yi zuzzurfan tattaunawa game da shawarwarin da haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙungiyoyin Arewa ta 'Coalition of Northern Groups (CNG)' ta bayar.
Sanarwar ta yi ƙarin haske da cewa, haɗaɗɗiyar ƙungiyar 'yan Arewar ta gudanar da wani taro ne na kwana biyu a Abuja a ranar 23 ga watan Janairun 2024, wanda tsohon shugaban ƙasa, Janar Abdussalami Abubakar ya shugabanta.
Sanarwar ta Idris ta ce, “jiya Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara da Gwamna Dikko Umar Raɗɗa na jihar Katsina sun gana da Ministan tsaro Badaru Abubakar a ma'aikatar tsaro da ke Abuja.
“Gwamnonin sun tattauna muhimman batutuwan da suka shafi tsaro a jihohin biyu, tare da samar da hanyoyin bi, bisa haɗin gwiwa da ma'aikatar tsaron don magance matsalar.
“Bayan zaman da ya gudana ma'aikatar rsaron, sai Gwamnonin biyu tare da Ministan tsaron, suka wuce zuwa ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro don gudanar da wani zaman na musamman.
“A wannan zaman tattaunawar ne suka amince da shawarwarin da aka bayar da wancan taro, wanda haɗaɗɗiyar ƙungiyar 'yan Arewar ta bayar.
“A cikin watan Janairun shekarar nan ne haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙungiyoyin Arewa ta gabatar da wani taron tattaunawa, wanda tsohon shugaban ƙasa, Janar Abdussalami Abubakar, tare da halartar wasu fitattun masu ruwa da tsaki daga yankin Arewacin ƙasar nan.
“Aiwatar da waɗannan shawawarin da wannan kwamiti na tsaro ya bayar, zai taimaka matuƙa wajen magance wannan tsalar tsaro mai rikitarwa da ta addabi Arewa Nijeriya.
“Wannan na cikin dabarbaru da haɗin gwiwar da waɗannan gwamnoni na Zamfara da Katsina suke bi don ganin sun kawo ƙarshen 'yan bindiga a jihohin su.
Wakilan wannan Ƙungiya ta 'Coalition of Northern Groups (CNG)' na cikin wannan tattaunawa da aka yi, bisa wakilcin shugaban kwamitin amintattu na Ƙungiyar, Nastura Ashiru Shariff; shugaban kwamitin tsaro na ƙungiyar, Alhaji Bashir Yusuf; Alhaji Ibrahim Ahmed Katsina; Janar Sarkin Yaki Bello, Ambasada Buhari Bala da Janar Sa'ad Abubakar.