Gwamnatin Jihar Katsina Ta Kaddamar da Raraba Tallafin jinkai ga wadanda Ambaliyar Ruwa ya Shafa.
- Katsina City News
- 15 Oct, 2024
- 220
Muhammad Aliy Hafiziy, Katsina Times
A ranar Asabar 15 ga watan Oktoba, 2024, Hukumar Kula da bada agajin gaggawa ta Jihar Katsina (SEMA), karkashin jagorancin Hajiya Binta Husaini Dan Gani, ta kaddamar da taron rarraba tallafin agaji ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa. Taron ya gudana a tsohon gidan gwamnati tare da halartar manyan jami'ai, ciki har da gwamna Malam Dikko Umar Radda na jihar Katsina, mataimakin gwamna Hon. Faruk Lawal Jobe, da sauran masu ruwa da tsaki.
Hajiya Binta ta bayyana tsare-tsaren tallafin, inda ta ce, wadanda gidajensu suka ruguje gaba daya za su karbi naira 600,000, yayin da masu gidajen da wani bangare ya lalace suka sami naira 300,000.
Gwamna Dikko Umar Radda ya jaddada cewa makasudin ambaliyar sun hada da rashin tsarin magudanar ruwa da gina gini ba tare da ka'ida ba, a kan hanyoyin ruwa. Ya tabbatar wa jama'a cewa gwamantin jihar na aiki tukuru don magance wadannan matsaloli ta hanyar tantance wuraren da ke da matsala don shigar da ingantaccen tsarin magudanar ruwa.
Gwamnatin Jihar Katsina ta bayar da taimako ga fiye da mutane 1,067 da ambaliyar ta shafa, inda aka rarraba kayan gini ga mutane 1,472 don gyaran gidaje. Bugu da kari, mutane 439 za su karbi naira 600,000 kowanne, yayin da 639 da gidajensu suka lalace za su karbi naira 300,000 a cikin asusun bankinsu.
Gwamna Radda ya nuna damuwarsa game da tasirin ambaliyar, yana mai cewa yankuna da dama da Ambaliyar ta shafa ba su da ingantaccen tsarin magudanar ruwa kuma suna bin hanyoyin sake ingantawa. Ya bayyana cewa an tanadi naira miliyan 293 don inganta tsarin magudanar ruwa a cikin kananan hukumomin da ambaliyar ta shafa.
Ya ce, "Kowanne mutum a Katsina ya shaida kokarinmu na gina manyan tsarin magudanar ruwa, wanda ya rage illolin ambaliyar a birnin, wanda ya ci gaba da kashe fiye da naira biliyan 10 a mataki na biyu na aikin." Hakanan, ya nuna cewa ingantawar hanyoyin a Kananan Hukumar Jibiya ta taimaka wajen rage hadarin ambaliyar ruwa.
Gwamnan ya jaddada himmarsu na ci gaba da kokarin inganta rayuwar al’ummar jihar. Taron tallafin, wanda aka gudanar a ofishin SEMA, ya samu halartar manyan jami’ai da masu ruwa da tsaki, yana nuna kudurin gwamantin na tallafawa al’ummar da ambaliyar ta shafa tare da tabbatar da sun karbi dukkanin taimakon da suke bukata.