CIBIYAR NAZARI DA BADA HORO AKAN AIYUKAN JINKAI DA BUNKASA RAYUWAR AL'UMMA TA KASA TA BA GWAMNAN JIHAR KATSINA, DIKKO RADDA LAMBAR YABO
- Katsina City News
- 14 Oct, 2024
- 403
A ranar Asabar, 12/10/2024 Cibiyar Nazari da Bada Horo Akan
Aiyukan Jinkai da Bunkasa Rayuwar Al'umma ta Kasa wato, Institute of Humanitarian Studies and Social Development (IHSD) ta karrama Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON tare da ba shi lambar yabo.
An mika lambar yabon ce a wajen bukin yaye daliban Cibiyar karo na 14 da Cibiyar ta gudanar da hadin guiwar Cibiyar Bada Horo da Gudanar da Bincike ta Majalissar Dinkin Duniya wato United Nations Institute for Training and Research- UNITAR a zauren taro na tunawa da Marigayi Janar Shehu Musa Yar'adua dake Abuja.
Da yake mika lambar yabon a madadin Cibiyar, shugaban taron kuma tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Dr. Mukhtar Ramalan Yero ya karanto cewa Cibiyar ta zabi Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON a matsayin Gwarzon Gwamna na bana a fannin kirkiro aiyukan jinkai da bunkasa rayuwar al'umma.
IHSD ta yi bayanin cewa, Gwamna Dikko Radda ya yi fice wajen kokarin maido da zaman lafiya da bullo da shirye - shiryen dake da nufin inganta walwala da ci gaban al'umma.
Cibiyar ta kuma baiwa Gwamnan takardar shedar karramamawa ta zama Babban Wakilinta wato, "Associate Distinguished Humanitarian Fellow" (ADHF).
Da yake jawabi gabanin karbar lambar yabon, Gwamna Dikko Radda wanda, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Garba Faskari ya wakilta, ya taya Cibiyar murnar bukin yaye dalibanta karo na 14.
Gwamnan ya ce, hakan yana nuni da irin nasarorin da IHSD din ke samu wajen horas da Jami'an gwamnati da na hukumomi masu zaman kansu akan muhimman dabarun inganta aiyukan su ta yadda za su amfani al'umma.
Ya ce bayanan aikace - aikacen da ta yi a baya ya nuna cewa ta yi nasara wajen horas da kwararru a fannonin aiyukan jinkai da kyautata jin dadin jama'a.
Malam Dikko Umaru Radda ya ce, a dalilin hakan ne Gwamnatin Jihar Katsina ke fatar cewa yarjejeniyar hadin guiwar da za ta kulla da Cibiyar, zai taimaka ma ta wajen aiwatar da sababbin manufofin da ta zo da su don bunkasa tattalin arzuki da walwala da jin dadin al'ummar Jihar.
Ya kuma yi godiya akan lambar yabon da Cibiyar ta ba shi wadda ya ce, ta zama kalubale gare shi na ya kara kaimi wajen kokarin kyautata rayuwar al'ummar Jiharsa.
A jawabin sa, shugaban hukumar zartarwar Cibiyar tsohon Jakadan Nigeriya a kasar Guinea kuma tsohon Kwamishinan kudi na Jihar Katsina, Ambasada Adamu Babangida Ibrahim ya ce IHSD wacce take aiki a karkashin kudurin Majalissar Dinkin Duniya tana bada horo ga Ma'aikatan gwamnati, da kwararru da Jami'an Kamfanoni da masu son kafa sana'o'i da za su kawo saukin rayuwa ga al'umma.
Ambasada Adamu Babangida ya ce Cibiyar, tana kuma shiga gaba wajen hada Mahalartanta da cibiyoyin kudi da Kungiyoyin Duniya masu bada tallafi kyauta ga masu sha'awar kafa sana'o'i don ci gaban al'umma.
Gwamnan Jihar Osun Sanata Ademola Adeleke na daga cikin wadanda Cibiyar ta karrama da lambar yabo ta bana.
Bunkin ya samu halartar muhimman mutane da suka hada da wakilyar Gwamnan Jihar Osun, Mrs Adenike da Sakatariyar hukumar zabe ta kasa INEC Mrs Rose Oriaran da wakilin DG na NYSC Bigadiya Janar YB Ahmed da wakilyar UNITAR a Nijeriya da tsohuwar Babbar Sakatariya a Ma'aikatar Harkokin Kasashen Waje ta Nijeriya, Mrs Anthonia Ekpa da Furofesa Chinwe Christopher daga Jami'ar 'West Cape', a Afirika ta Kudu.
Sauran sun hada da Mahalarta horon da aka yaye da kuma sababbin da Cibiyar ta dauka a bana wadanda cikinsu akwai, Masana da Shugannin Kamfanoni da Kwararru daga bangarori rayuwar al'umma daban.
Daga cikin abubuwan da suka kayatar a wajen taron akwai, kaddamar da littattafai guda biyu masu suna "A STUDY OF ETHNICITY AND RELIGION AS DRIVERS OF CONFLICT IN AFRICA" da kuma "ADVERSE INFACTS OF HUMANITARIAN CRISIS ON WOMEN AND CHILDREN" wadanda Magatakardar Cibiyar Ambasada Prince Francis Origa ya wallafa.
Abdullahi Aliyu Yar'adua,
Director Press,
SGS Office, Katsina.