Katsina United da Rivers United Sun Tashi Diro a Gasar NPFL
- Katsina City News
- 13 Oct, 2024
- 319
Katsina Times
A yau a filin wasa na Muhammad Dikko da ke Katsina, an kammala wasan tsakanin Katsina United da Rivers United a matakin wasannin mako na shida na gasar Premier ta Najeriya (NPFL), inda aka tashi kunnen doki 0-0.
An yi shiru sosai a farkon wasan har zuwa minti na 50, lokacin da Katsina United ta samu bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan wani laifi da aka yi musu, amma Mansoor Saleh ya buga kwallon bai kai inda ake so ba. An kasa zura kwallo a raga.
A minti na 66, Katsina United ta fara musanya 'yan wasa, inda ta maye gurbin Nazifi Yahaya da Taofeeq Ahmed da Boslam Dawi da Innocent Kingsley, amma duk da haka an kasa karya kwalliyar duka bangarorin.
Ismael Muhammad daga Katsina United ya samu katin gargadi a minti na 70 bayan ya hana Rivers United kai farmaki mai hatsari.
A karshen minti na 80, Katsina United ta yi musanya na gaba, inda Muhammad Ibrahim da Peculiar Iheme suka bar fili, aka shigar da Moses Achare da Nafi’u Ibrahim Kangiwa. An samu damar kai hari ta hannun Nafi’u Ibrahim, wanda ya bai wa Moses Achare kwallo amma bai samu damar cin kwallon ba, saboda babu wani dan wasan Katsina United a kusa da kwallon.
Wasan ya kare 0-0, duk da kokarin da aka yi a bangarorin biyu na neman zura kwallo a raga, amma dukkan kungiyoyi sun gaza samun nasara a wannan wasa mai zafi na gasar NPFL.