Jawabin Shugaba Bola Tunubu Na Ranar 'yanci da Harshen Hausa.
- Katsina City News
- 01 Oct, 2024
- 421
Fassarar Rahama Abdulmajid
Ya ku ’yan Najeriya..
Ina muku wannan jawabin ne a yanzu, cike da masaniyar fadi-tashin da akasarinku ke yi da
da halin matsin da muka sami kanmu a ciki a wannan mawuyacin lokaci.
Gwamnatinmu ta kwana da sanin yadda yawancinku ke fama da tsadar rayuwa da neman aikin-yi. Ina mai tabbatar maku da cewa muryoyin ku na isowa gare ni.
A matsayina na shugaban ku, ina tabbatar muku cewa, tuni muka bazama wajen neman mafita mai dorewa ga radadin da ‘yan kasarmu ke ciki.
A wannan karon ma, roƙon ku zan kara yi, ku yi haƙuri, ku kara juriya domin a bangaren garambawul din da muka dauko, tuni, muka fara hango yadda hakar mu ta fara cimma ruwa.
Shekaru 64 cif kenan, da kakanninmu suka kafa mulkin dimokuradiyya a kasarmu, kuma suka kaddamar da burin samar da babbar kasa da za ta fitar da sauran kasashen Afirka daga kangin talauci, jahilci, da koma-baya, suka mayar da kasarmu wata fitila da ke haskaka fata na gari ga sauran kasashen Afirka da ma duniya baki daya.
Da za mu waiga shekaru sittin baya, ilahirin ’yan Najeriya dake fadin duniya za su iya ganin yadda wasu daga cikin manyan mafarkan iyayenmu suka fara tabbata.
Daukacin duniya na fa'idantuwa da ruhin jajircewar al'ummar Najeriya, da tarin baiwar ƙwararrunmu a kowane fanni ciki har da kasuwancinmu da masana'antarmu a har zuwa kan kimiyya da fasaha da abubuwan more rayuwa. Aikin tabbatar da hasashen kakanninmu abu ne da zamu ci gaba da yi a kowace rana, har sai mun tabbatar da mun aiwatar da shi fiye da zatonsu.
Duk da yake abu ne mai kyau mu ringa duba kura-kuran mu na baya, da kuma wuraren da muka yi tuntuɓe a matsayin mu na ƙasa, amma duk da haka bai kamata mu manta da nisan da muka yi wajen ginawa da kuma riƙe ƙasarmu tare ba.
Tun bayan samun 'yancin kai, kasar mu ta tsira daga rikice-rikice irin wadanda da suka haifar da wargajewar kasashe da dama a duniya. Shekaru shida bayan samun 'yancin kai, ƙasarmu ta shiga cikin rikicin siyasa wanda ya haifar da yaƙin basasa mai zafi kuma wanda za a iya guje masa. Amma bayan mun fita daga cikin wancan mummunan lokaci, mun koyi rungumar bambance-bambancenmu da kuma sarrafa sabaninmu cikin hikima yayin da muke ci gaba da aiki wajen samarwa da kanmu kyakyawar kasa.
Duk da ɗimbin ƙalubalen da suka addabi ƙasarmu, mun kasance ƙasa mai ƙarfi, haɗin kai, kuma mai cin gashin kanta da tarin albarka.
Ya ku ’yan uwa, bikin murnar zagayowar ranar samun ’yancin kai, ya sake ba mu damar yin tunani kan irin nisa da muka yi a wannan tafiya tamu ta gina kasa da kuma sabunta alkawarinmu na gina kasa mai inganci, wadda za ta yi hidima ga al’ummar Nijeriya na yanzu da ma na gaba.
Yayin da muke murnar ci gaban da muka samu a matsayin mu na al'umma cikin shekaru sittin da huɗu da suka gabata, dole ne mu kuma gane wasu daga cikin damarmakin da muka rasa da kuma kura-kuran da muka yi a baya. idan dai zamu zama ɗaya daga cikin manyan ƙasashen duniya, kamar yadda Allah Ya ƙaddara mana, kura-kuranmu ba su kamata su biyo mu zuwa gaba ba."
Gwamnati na, ta karɓi shugabancin ƙasarmu watanni 16 da suka gabata a wani mawuyacin hali. Ga kuma tattalin arzikinmu na fuskantar matsaloli da dama, hadi da tabarbarewar al’amuran tsaron lafiyarmu. Mun tsinci kanmu a wata mararraba mai cike da rudani, inda dole ne mu zabi tsakanin hanyoyi biyu: gyara domin samun ci gaba da wadata ko ci gaba da tafiyar da lamura kamar yadda suke har mu durkushe. Muka yanke shawarar gyara tattalin arzikin mu a siyasance da kuma gina fasalin tsaro..
A bangaren tsaro ina mai farin cikin sanar da ku ’yan uwana cewa gwamnatinmu tana samun nasara a yaki da ta’addanci da ‘yan fashin daji. Burinmu shi ne mu kawar da duk wata barazana ta Boko Haram, da ‘yan fashi daji, da kuma masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, da kuma duk wani nau’i na ta’addanci. A cikin shekara guda gwamnatinmu ta kawar da kwamandojin Boko Haram da ‘yan fashin daji cikin sauri fiye da kowane lokaci. A kididdigar baya-bayan nan, sama da kwamandojin Boko Haram 300 da na ‘yan ta’addan daji dakarun sojojin mu a yankin Arewa maso Gabas, da Arewa maso Yamma, suka hallaka.
Mun dawo da zaman lafiya a daruruwan garuruwan Arewa, yayinda dubban al’ummar mu suka koma muhallansu. Ba kuma nan aka tsaya ba, jami’an tsaron mu na cigaba da dukufa wajen kawo karshensa cikin gaggawa. Da zaran mun dawo da zaman lafiya a yawancin garuruwan yankunan Arewa da ke fama da rikici, manoman mu za su iya komawa gonakinsu. Muna sa ran ganin ci gaba mai ƙarfi a fannin samar da abinci da kuma raguwar farashin kayan abincin. Ina mai yi maku alkawari, ba za mu yi kasa a guiwa ba a kan wannan."
Gwamnatinmu tana daukar matakan shawo kan bala'o'in da suka faru a baya-bayan nan, musamman ma ambaliyar ruwa a sassan kasar nan. Bayan da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ziyarci Maiduguri, nima kuma na kai ziyara domin tabbatar wa al’ummarmu cewa gwamnatin tarayya za ta kasance tare da al’umma a duk lokacin da suke cikin mawuyacin hali. A taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya na karshe, mun amince da samar da Asusun Ba da Agajin gaggawa don tara kudade daga jama’a da kuma kamfanoni masu zaman kansu da zai taimaka mana wajen samar da taimakon gaggawa.
Gwamnatinmu ta kuma ba da umarnin a yi gwajin inganci a dukkan madatsun ruwa na kasar nan don gujewa bala'i a nan gaba.
Tattalin arzikin kasar yana fuskantar gyare-gyare da sabbin tsare-tsare domin ya zama mai amfani da dorewa. Idan ba mu gyara kura-kuran kasafin kuɗi da suka jawo koma bayan tattalin arziki ba, ƙasarmu za ta fuskanci makoma marar tabbas da haɗarin hasara maras misaltuwa."
Saboda gyare-gyaren da aka yi, kasar ta samu sanya hannun jari na kai tsaye daga kasashen ketare da ya kai sama da dala biliyan 30 a shekarar da ta gabata.
"'Yan'uwana 'yan ƙasa, gwamnatinmu ta kuduri aniyar tabbatar da kasuwancin 'yanci, shiga kyauta, da fita kyauta a cikin jarin kasuwanci, yayin da muke kula da daraja da kuma tasirin hanyoyin gudanarwarmu. Wannan ka'idar ce zata jagoranci cinikayyar raba hannun jari a cikin kasuwancin hakar man fetur na kasar nan, a kokarin mu na jajircewa wajen inganta arzikinmu. Don haka ne ma, kamfanin , ExxonMobil Seplat divestment zai sami amincewar ministoci cikin 'yan kwanakin nan, bayan hukumar NUPRC ta kammala sahalewa , bisa ga dokar masana'antar man fetur ta PIA. kamar yadda aka saba wajen amincewa da saka a hannun jari a bangaren.
wanna matakin zai kara habakawa da kuma kara yawan man fetur da iskar gas, hakan kuma zai yi tasiri ga habakar tattalin arzikinmu.
Ingantacciyar hanyar da Babban Bankin kasa CBN ya ɗauka don tafiyar da manufofin kuɗi, ya tabbatar da kwanciyar hankali da tsinkaya a kasuwar musaya ta kudaden ketare. Mun gaji ajiyar sama da dala biliyan 33 watanni 16 da suka gabata. Tun daga wannan lokacin, mun biya bashin dala biliyan bakwai da muka gada. Mun kawar da bashin sama da Naira tiriliyan 30. Mun rage nauyin bashi da ke kan mu daga kashi 97 zuwa kashi 68 cikin 100. Kuma duk da haka, mun yi nasarar ajiye dala biliyan 37 a asusun ajiyar mu na ketare. yayin da a hakan muke cigaba da da gudanar da abubuwan da suka rataya a wuyanmu
Mun kuma cigaba da aiwatar da gyare-gyaren manufofin kasafin kuɗi. kazalika muna cigaba da inganta samar da kayayyaki da kuma ƙirƙirar ƙarin ayyuka da wadata. Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da kudirorin Tabbatar da Tattalin Arziki, wanda za a miƙa su ga Majalisar Tarayya. Wadannan kudirorin sauyin za su inganta yanayin kasuwanci ya zama mai kyau, su kuma karafafa gwiwar saka hannu jari, da kuma rage nauyin haraji ga kamfanoni da ma'aikata idan an amince da su a matsayin doka."
A matsayin wani bangare na kokarinmu na sake farfado da tattalin arzikinmu a siyasance, da gaske muke wajen aiwatar da hukuncin da kotun koli ta yanke kan cin gashin kai ga harkokin kudi na kananan hukumomi.
Babban abin da ke damun mutanenmu a yau shi ne tsadar rayuwa, musamman tsadar abinci. kuma matsala ce da ke damun mutane da yawa a ko'ina, yayin da farashin kayayyaki da tsadar rayuwa ke ci gaba da tashi a duk faɗin duniya
’Yan uwana ’yan Najeriya, ina baku tabbacin cewa, muna aiwatar da matakai masu yawa don rage tsadar rayuwa a nan gida.
Ina yabawa Gwamnonin musamman na Kebbi, Neja, Jigawa, Kwara, Nasarawa, da Gwamnonin Kudu maso Yamma da suka rungumi shirin noma. Ina kira ga sauran jihohi da su hada hannu da Gwamnatin Tarayya wajen saka hannun jari a harkar noma. Muna ba da gudummawarmu ta hanyar samar da taki da samar da taraktoci da sauran kayan aikin gona. A makon da ya gabata ne Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da kafa cibiyar hada taraktoci na John Deere 2000, da zata samar da na’urorin girbi da na huda, garma har ma da sauran kayan aikin gona. Ana kuma sa ran kammalawa cikin watanni shida.
A yanzu haka ana kan aiwatar da fadada shirin shugaban kasa na chanzawa ababan hawanmu makamashi zuwa amfani da iskar gas na CNG, musamman domin sufurin jama'a ta hanyar hada hannu da kamfanoni masu zaman kansu. Gwamnatin Tarayya a shirye take don taimaka wa jihohi 36 har da babban birnin tarayya wajen sayen motocin CNG don sauƙaƙe sufuri na jama'a.
’Yan uwa ’yan Najeriya, yayin da muke aiki don tabbatar da ingantaccen tattalin arziki da tsaron ƙasa, muna kuma neman ƙarfafa haɗin kai na ƙasa da gina zaman lafiya da haɗin kai a cikin al'umma. Tattalin arzikinmu na iya bunƙasa ne kawai idan akwai zaman lafiya."
Yayin da muke aiki domin shawo kan kalubalen yau, muna kuma ci gaba da tunanin ƙarni na gaba yayin da muke ƙoƙarin ƙarfafa kaifin tunaininsu domin kyakkyawan makoma. Muna jagorantar yau tare da hangen nesa na makomar da muke son bar wa jikokinmu, tare da gane cewa ba za mu iya tsara makoma da ta dace da su ba, ba tare da sanya su a matsayin masu gina ta ba
La’akari da haka ne ma, nake farin cikin sanar da taron Matasa na Kasa. Wannan taron zai zama wani dandali na tattauna kalubale da dama da ke fuskantar matasanmu, wadanda suka kai sama da kashi 60 cikin 100 na yawan al'ummar mu. Zai haifar da tattaunawa mai ma'ana da kuma bawa matasanmu damar shiga cikin gina ƙasa. Ta hanyar tabbatar da cewa an ji muryoyinsu a cikin tsara manufofin da ke shafar rayuwarsu, ta haka ne zamu samar da hanyar da za ta kasance mai haske a gobe.
babban taron matasan na kwanaki 30, zai hada kan kafatanin matasan kasar, sa za su yi hadin gwiwa domin samar da mafita ga matsaloli kamar ilimi, aikin yi, kirkire-kirkire, tsaro, da adalci na zamantakewa. Za a samar da wani tsarin fitar da wakilai tare da tuntuɓar matasanmu ta hanyar wakilansu. Ta hanyar babban taron matsan na kasa, zai zama aikinmu a matsayin shugabanni, mu tabbatar da abinda ke damun matasan shine zai kasance muhimmin abun tattaunawar a taron. Gwamnati za ta yi la'akari sosai tare da aiwatar da shawarwari da sakamakon da aka samu daga wannan dandalin yayin da muke ci gaba da jajircewa kan manufofinmu na gina kasa mai dunkulewa, wadata, da hadin kai.
Gwamnatinmu na cigaba da aiwatar da wasu tsare-tsare da dama da suka shafi matasa don baiwa matasanmu damar samun ci gaba a duniya mai saurin canzawa. Wasu daga cikin abubuwan da muke aiwatarwa domin matsan sun hada shirin 3MTT na Ma'aikatar Sadarwa, Ƙirƙira da Tattalin Arzikin yanar gizo, da nufin gina ginshikin basirar fasaha na Nijeriya.
Mun kuma aiwatar da Asusun Ba da Lamuni na Ilimi na Najeriya (NELFUND), wanda ke ba da lamuni mai arha ga ɗalibanmu don cin ma burinsu na karatun gaba da sakandare. Bugu da kari, a karshen wannan watan, za mu kaddamar da The Renewed Hope Labor Employment and Empowerment Programme (LEEP). Ma’aikatar Kwadago da Ayyuka ta Tarayya ta yi la’akari da shi da nufin samar da ayyukan yi miliyan 2.5, kai tsaye da kuma a kaikaice, a kowace shekara, tare da tabbatar da walwala da amincin ma’aikata. a fadin kasar.
Kamar yadda aka saba bisa al’ada, nan ba da jimawa ba gwamnati za ta sanar da duk wadanda za’a karrama da lambar yabo ta kasa.
Za’a karrama shugaban majalisar dattawa da alkalin alkalai na tarayya da lambar karramawa ta babban kwamandan odar Niger wato GCON. Sai Mataimakin shugaban majalisar dattijai da kakakin majalisar wakilai da za’a karrama da lambar yabo ta Kwamandan Tarayyar Najeriya wato CFR, yayin da mataimakin kakakin majalisar wakilai za’a karrama shi da lambar yabo ta Kwamandan odar Niger waro CON .
’Yan uwa ’yan Najeriya, kwanaki masu kyau na tafe. Kamata yayi kalubalen da muke fuskanta a yanzu ya sa mu kara amincewa da kawunan mu a ko da yaushe. Mu 'yan Najeriya ne - masu juriya da jajircewa. Mun saba farfadowa daga kowanne irin hali muka tsinci kanmu.
Ina rokonku ku da ku yarda da alkawarin ƙasarmu. Hanyar da ke gabanmu ka iya zama mai ƙalubale, amma za mu samar da hanya zuwa ga kyakkyawar makoma tare da goyon bayanku. Tare, za mu haɓaka Nijeriya da ta dace da muradan dukkan 'yan ƙasa, ƙasa mai ƙima, girmamawa, da nasara ta haɗin gwiwa."
A matsayinmu na wakilan canji, za mu iya tsara makomarmu kuma mu gina kyakkyawar makoma da kanmu, domin kanmu, domin jikokinmu.
Ku taimaka ku shigo gwamnatinmu a wannan tafiya zuwa ga kyakkyawar makoma. Mu yi aiki tare don gina Nijeriya mai girma wadda kowanne ɗan ƙasa zai samu damarmaki, kuma kowanne yaro zai girma da fata da alkawari."
Allah ya ci gaba da yiwa al'ummar mu albarka, ya kuma kiyaye jami'an tsaron mu.
Barka da ranar samun 'yancin kai, 'yan uwana 'yan Najeriya!